Peter Obi ya lashe zaɓe a jihohi 11 da Abuja

Sakamakon shugaban ƙasar da ake ci gaba da tattarawa a Najeriya ya nuna cewa ɗan takarar jam'iyyar Labour Peter Obi ya samu nasara a jihohin ƙasar bakwai.
Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya samu nasara a jihohin Legas da Abuja da kma Plateau da sauransu.
Ga jerin jihohin da mista Obi ya lashe kawo yanzu:
ENUGU:
APC 4,772
LP 428,640
NNPP 1,808
PDP 15,749
LAGOS:
APC 572,606
LP 582,454
NNPP 8842
PDP 75750
ABUJA
APC - 90,902
LP - 281, 717
PDP - 74,194
NNPPN - 4,517
EDO
LP 331,163
APC 144,471
PDP 89,585
NNPP 2,743
ABIA
LP - 327,095
PDP - 22,676
APC - 8,914
NNPP - 1239
PLATEAU
PDP - 243,808
APC - 307,195
LP - 466,272
NNPP - 8,869
NASARAWA
APC- 172,922
LP- 191, 361
PDP-147,093
NNPP-12,715
CROSS RIVER
LP - 179, 917
APC - 130,520
PDP - 95,425
NNPP - 1,644
DELTA
APC - 90,183
LP - 341,866
NNPP - 3,122
PDP - 161,600
EBONYI
APC - 42,402
LP - 259,738
NNPP - 1, 661
PDP - 13, 503
ANAMBRA
APC - 5,111
LP - 584,621
NNPP - 1,967
PDP - 9, 036
Sai dai Tinubu ya samu nasara a jihohi uku cikin da aka bayyana sakamakonsu kawo yanzu - watau jihohin Kwara da Ekiti da kuma Ondo.
Amma jinkirin da ake samu wajen samun sakamakon zaɓen na sanya mutane cikin damuwa.
Hukumar zaɓen ƙasar ta nemi afuwa kan rashin sanya sakamakon zaɓe daga mazaɓu a shafinta na intanet, tana mai cewa an samu matsalar nau’rar ne saboda yawan mutanen da suke ƙoƙarin shiga domin samun bayanai.
A zaɓen shekarar 2019, Peter Obi ne ya yi wa Atiku Abubakar mataimaki a takarar shugaban ƙasa a ƙarkashin jam'iyyar PDP.











