Arsenal za ta ɗauki Joan Garcia, Everton na bibiyar Amrabat

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal za ta ƙara ƙaimi a ƙoƙarin ta na sayen mai tsaron gidan Espanyol kuma ɗan Sifaniya mai shekara 23, Joan Garcia, yayin da nata mai tsaron gidan kuma ɗan Ingila mai shekara 26, Aaron Ramsdale ke shirin komawa Southampton kan kuɗi £25m. (Athletic - subscription required)
Ɗan wasan gaban Najeriya mai taka leda a Napoli Victor Osimhen, mai shekara 25 da Chelsea ta daɗe ta na zawarci ya samu tayin kwangilar shekara huɗu kan £25m kowacce shekara, daga ƙungiyar Al-Ahli ta babbar gasar Saudiyya (Sky Sports)
Ɗan wasan gefen Ingila mai shekara 24, Jadon Sancho, na shirin sauya sheƙa zuwa Juventus daga Manchester United a matsayin aro. (RMC Sport)
Aston Villa za ta shiga cinikin ɗan wasan gaban Roma da Ingila, Tammy Abraham mai shekara 26, idan ɗan wasan gabanta ɗan Colombia mai shekara 20 ya bar ƙungiyar kafin lokacin rufe kasuwar cinikin ƴan wasa. (Football Insider)
Crystal Palace ta cimma matsaya da Wolfsburg kan cinikin ɗan wasan bayan Faransa mai shekara 24, Maxence Lacroix, a matsayin wanda zai maye gurbin ɗan wasan bayan Denmark mai shekara 28, Joachim Andersen wanda ya koma Fulham. (Sky Sports)
Liverpool ta ƙi amincewa da tayin da Bayer Leverkusen ta gabatar mata a kan ɗan wasan Ingila mai shekara 21, Tyler Morton. (Sky Sports)
Newcastle United na zawarcin mai tsaron gidan Burnley kuma ɗan tawagar matasan Ingila, James Trafford. (Football Insider)
Everton ta tuntuɓi Fiorentina kan ɗan wasan tsakiyar Morocco, Sofyan Amrabat, mai shekara 28, wanda ya shafe kakar wasan bara a matsayin aro a Manchester United. (Talksport)
Ɗan wasan bayan Manchester City mai shekara 23, kuma ɗan Burkina Faso, na shirin komawa taka leda a Benfica a matsayin aro. (Sky Sports)
Fulham na zawarcin ɗan wasan tsakiyar Lyon mai shekara 20, kuma ɗan ƙasar Ghana, Ernest Nuamah. (Athletic - subscription required)












