Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Iƙirarin Rasha da Ukraine kan iko da birnin Soledar
Rundunar sojojin haya ta ƙasar Rasha wato Wagner Group ta yi iƙirarin ƙwace iko da garin Soledar da ke gabashin Ukraine - sai dai Ukraine ta ce sojojinta suna nan riƙe gam da birnin.
Kafar watsa labarai ta Rasha ta ɗauki wata sanarwa wadda ake ganin shugaban Wagner Yevgeniy Prigozhin ne ya fitar wanda ya ce an yi wa Ukraine ɗin ƙawanya.
Mataimakiyar ministan tsaro ta Ukraine Hanna Maliar tun da farkta bayyana cewa "ana ci gaba da musayar wuta mai ƙarfi".
Iƙirarin da duka ɓangarorin ke yi kan cewa suna da iko da birnin duka ba a tantance ko tabbatar da shi ba.
A sanarwar da aka bayar da rahoton da aka fitar a ranar Talata, Mista Prigozhin ya bayyana cewa: "Rundunar Wagner ta ƙwace iko da da duka yankin Soledar. An yi wa birnin ƙawanya ta ciki inda ake ci gaba da yaƙi a cikin garin."
Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin Wagner ne kawai waɗanda ba su cikin rundunar sojin Rasha su ne suke cikin masu kai hari Soledar.
A ɗayan ɓangaren, Ms Maliar ta bayyana cewa sa'o'i kafin nan, "abokan gaba sun daina mayar da hankali kan mutanensu da ke mutuwa tare da ci gaba da kai hari," in ji ta.
Ƙwace garin Soledar - wanda ƙaramin gari ne da ake haƙo gishiri a yankin Donetsk - zai iya taimaka wa dakarun Rasha zagaye birnin Bakhmut.
Birtaniya a ranar Talata ta bayyana cewa dakarun Rasha da kuma sojojin haya na Wagner akwai yiwuwar su ci gaba da iko da garin.
A ranar Litinin, Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce babu kusan kowa da ya rage a Soledar kuma babu wani bango da ya rage.
"Wannan shi ne abin da hauka ke nufi," in ji shi. Haka kuma a wani sabon jawabi da ya yi a ranar Talata da dare, Mista Zelensky ya jinjina wa ƙoƙarin dakarun Ukraine.
Haka kuma a wani sabon jawabi a ranar Talata, Mista Zelensjy ya jinjina wa dakarun Ukraine.
Ana muhawara a kan muhimmancin Soledar, amma ƙwace iko da garin zai zama yana da muhimmanci kan abubuwa biyu. Na farko shi ne dakarun Rasha sun ƙara matsawa kusa da birnin Bakhmut.
Rasha za ta iya amfani da birnin Soledar kamar wurin haƙar gishiri da ramuka na ƙarƙashin ƙasa waɗanda suke wurin tun watan Afrilun bara domin shiga cikin yankin da Ukraine ke da iko da shi.
Na biyu kuma dakarun da suka kutsa cikin Ukraine za su iya saka Ukraine ɗin ta ɗanɗana kuɗarta.
Wani abu da ya taimaka wa Ukraine ta ci gaba da iko da yankunanta shi ne yadda take kai farmaki kan kayayyakin da Rasha ke jigila na yaƙi.
Ƙwace iko da garin Soledar - wanda yake da kimanin mutum 10,000 kafin a soma yaƙin - zai iya sa birnin Bakhmut ya rasa samun muhimman kayayyaki daga Sloviansk.
Birtaniya ta bayyana cewa tana kyautata zaton birnin Soledar na daf da faɗawa hannun Rasha amma ta ƙara da cewa ba lallai bane Rashar ta ƙwace iko da Bakhmut sakamakon irin jajircewar Ukraine wurin kare birnin.
Wani babban jami'in sojan Amurka daga ma'aikatar tsaro ta Amurka ya bayyana cewa akwai wani sashe mai girma na Soledar da ke hannun Rasha.