Ƴan Birtaniya biyu sun yi ɓatan-dabo a Ukraine

An wallafa

'Yan sandan Ukraine sun ce wasu 'yan ƙasar Birtaniya biyu sun ɓace a yankin Donetsk da ke gabashin ƙasar.

Mutanen biyu masu suna Andrew Bagshaw, mai shekara 48 da Christopher Parry, mai shekara 28 suna aiki ne da ƙungiyoyin bayar da agaji, kuma 'yan sanda sun ce rabon da a gansu tun ranar Juma'a lokacin da suka nufi garin Soledar, inda faɗa ke kara tsananta.

Ma’aikatar harkokin wajen Birtaniya ta ce ‘‘tana taimaka wa iyalan mutanen’’.

Mahaifan mista Bagshaw sun ce suna ‘alfahari da duk irin ayyuka da yake yi’’ kuma suna ‘son sa matuka’.

Mr Parry, wanda ya fito daga garin Truro da ke Cornwall, ya yi tafiya zuwa Ukraine domin yin aikin agaji inda a baya-bayan nan yake taimaka wa mutane barin garin Bakhmut da ke gabashin birnin Donbas.

Da yake magana da BBC daga Ukraine lokacin bikin kirsimetin bara, ya bayyana kokarin da yake yi na taimaka wa mutane da kuma yadda yake jin dadin zama da mutanen.

Ya kuma yi magana kan ci gaba da harba bama-bamai a yankin da suke har ma wani jirgi maras matuki ya kusa faɗawa kusa da shi.

Mista Parry ya rubuta a shafinsa na intanet kan tara kuɗi don gyara motoci da sayen man fetur da kayaki domin taimakawa wajen kwashe fararen hula , inda ya bayar da misali da taimakawa a kwashe yara da kuma iyalai domin ficewa daga wajen da ake faɗa.

A wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a New Zealand – inda mista Bagshaw ke zama – iyayensa sun yaba da irin aikin da yake yi na ‘kai kayan abinci da magunguna da kuma taimaka wa tsofaffi barin wuraren da faɗa ya tsananta’’.

‘Yan sanda a birnin Bakhmut sun ce a ranar Asabar sun samu rahoton ɓatar mutane biyu da misalin 5:15 agogon ƙasar, inda suka buƙaci bayanai da za su taimaka wajen gano mutanen.

Mutanen biyu dai na a birnin Kramatorsk ne, inda aka samu rahotannin kai hare-hare a baya-bayan nan.

Tun da farko a ranar Litinin, rundunar sojin Ukraine ta ce tana ƙara ƙarfafa dakarunta a Soledar – wani ƙaramin gari kusa da Bakhmut – a wani yunkuri na kare kai daga hare-haren da sojojin haya na Rasha Wagner ke kaiwa.

Shugaban rundunar sojin ya sha alwashin kwato garin, mai albarkatun ma’adanai.

Maikatar  harkokin waje ta Birtaniya ta gargaɗi yan kasar su kiyayi zuwa Ukraine saboda hare-haren da ake kai wa birane daban-daban na kasar, yayin da mamayar da Rasha ta yi wa kasar ta shiga wata na 11.

Ma’aikatar ta ce akwai yiwuwar ‘’gamuwa da mummunan haɗari’’ ga rayukansu, kuma ta bukaci dukkan yan Birtaniya da suka rage a cikin ƙasar da su fice ba tare da ɓata lokaci ba.

A shekarar da ta gabata, 'yan Birtaniya da dama ne suka ɓace, yayin da aka kama wasun su.

A watan Satumban da ya gabata, wasu mayaƙa da Rasha ke mara wa baya suka sako wasu 'yan Birtaniya biyar bayan da Saudiyya ta ce ta shiga tsakani kuma ta kulla yarjejeniyar musayar fursunoni 10 na Rasha da Ukraine.   

Wannan na nufin an bar Aiden Aslin da John Harding da Dylan Healy da Andrew Hill da kuma Shaun Pinner dukkansu su koma gida bayan kama su na tsawon watanni.