Tsoffin ƴan Barcelona za su fafata da na Real Madrid a sada zumunta

Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Tsoffin ƴan wasan Barcelona za su kara da na Real Madrid ranar 15 ga watan Disamba a filin wasa na Ajinomoto a birnin Tokyo a Japan.

Tun kafin nan za su kece raini a birnin Doha a Qatar ranar 28 ga watan Nuwamba

Fitatcen ɗan wasan Barcelona, Andres Inesta, wanda ya yi ritaya, ya yi kaka biyar a Japan a ƙungiyar Vissel Kobe.

Wasu da za su yi wa Barcelona karawar har da Xavi, wanda ya horar da ƙungiyar da ɗan kasar Argentina, Javier Mascherano.

A karon farko ɗan kasar Mexico, Rafa Marquez, zai buga wasan, wanda ya horar da Barça Atletic kaka biyu.

Dukkan ƴan wasan huɗu za su sake sa rigar Barcelona a karon farko tun bayan 2018 da ya haɗa da Iniesta da Xavi tun bayan 2015 da Mascherano tun bayan 2018 da Marquez tun bayan 2010.

Sauran da za su kara a wasan na hamayya sun haɗa da Rivaldo da Bojan Krkic da Javier Saviola da Ludovic Giuly da Adriano da Gaizka Mendieta da sauransu.

Barcelona ta kirkiro ƙungiyar tsoffin ƴan wasa a 2016.