Arsenal na neman Diaz, Za a riƙa cin tarar Man Utd fam miliyan 90

Asalin hoton, Getty Images
Za a ci tarar Manchester United fam miliyan 10 a duk kaka, idan har kungiyar ta kasa samun gurbin zuwa gasar Zakarun Turai (Champions League), a karkashin yarjejeniyar fam miliyan 90 a duk shekara da suka kulla da kamfanin yin kayan wasa na Adidas. (Times)
Arsenal na shirin neman dan wasan tsakiya na Real Madrid Brahim Diaz kuma a shirye take ta biya har fam miliyan 60 a kan dan wasan mai shekara 24 wanda a kwanan nan ya koma tawagar Moroko. (Football365)
Manchester City ta tuntubi Newcastle United a game da dan wasanta na tsakiya Bruno Guimaraes dan Brazil mai shekara 26. (AS )
Liverpool na sha'awar sayen dan wasan tsakiya na Jamus Jamal Musiala, mai shekara 21, wanda kungiyarsa Bayern Munich ta yi masa farashin fam miliyan 100. (Football Insider)
Haka kuma ana danganta Liverpool din da neman sayen dan gaban Eintracht Frankfurt Omar Marmoush, na Masar mai shekara 25. (Bild, daga FourFourTwo)
Manchester City ta yarda da sayen matashin dan wasan gaba na gefe Savio, dan Brazil mai shekara 19, a bazara, wanda ke zaman aro a Girona, daga wata daga cikin kungiyoyin da ke da alaka da City din Troyes. (Football Insider)
Brentford da Aston Villa na son sayen dan wasan tsakiya na Bologna Lewis Ferguson, na Scotland, mai shekara 24. (TeamTalk)
Fulham na shirin gabatar wa dan bayanta na Ingila, Tosin Adarabioyo, sabon kwantiragi. (Mail)
A shirye Leeds United take ta saurari tayin sayen dan gabanta na gefe Jack Harrison, na Ingila wanda ya shafe kaka a zaman aro a Everton. (Football Insider)
Watakila Jurgen Klopp ya samu aikin horad da tawagar Jamus, ganin yadda suke neman yin sassauci ga kociyan wanda ke shirin barin Liverpool. (Football Transfers)
Rashin tabbas game da makomar Erik ten Hag a Manchester United, ya sa sauran ma'aikatan da ke aiki a karkashinsa cikin kila-wa-kala. (Mail)
Tattaunawa ta yi nisa da wani kamfanin Amurka ta Arewa don sayen kungiyar Reading. (Sky Sports)
Wolves na dab da kammala cinikin matashin dan wasan tsakiya na Rochdale, Matheus Mane, dan Ingila mai shekara 16, domin kungiyar renon 'yan wasanta (Fabrizio Romano)











