Saura maki ɗaya Liverpool ta lashe kofin Premier na bana

Premier League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Ƙungiyar Liverpool na fatan lashe kofin Premier League na bana da zarar ta samu maki ɗaya nan gaba a wasan da za ta buga.

Liverpool za ta karɓi bakuncin Tottenham a wasan mako na 34 a babbar gasar tamaula ta Ingila a Anfield ranar Lahadi 27 ga watan Afirilu.

Liverpool ta samu wannan damar ranar Laraba, bayan da Arsenal da Crystal Palace suka tashi 2-2 a Emirates a Premier League.

Hakan ya sa ƙungiyar Anfield ta ci gaba da zama ta ɗaya a kan teburi da maki 79, ita kuwa Arsenal, wadda take ta biyu take da maki 67.

Kenan Liverpool na bukatar koda canjaras ne, domin lashe babban kofin tamaula na Ingila na kakar nan kuma na 20 jimilla.

Manchester United tana da kofin Premier League guda 20 da take da shi jimilla.

Wannan shi ne karo na huɗu da za a fafata a bana tsakanin Liverpool da Tottenham, kuma na biyu a Premier League.

Liverpool ta je ta doke Tottenham 6-3 a Premier League ranar 22 ga watan Disambar 2024.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai karo biyun da suka fafata a League Cup, inda Tottenham ta ci 1-0 a wasan farko a daf da karshe, daga baya Liverpool ta ɗura 4-0 a wasa na biyu a Anfield.

Tottenham, wadda take ta 16 a kasan teburi da maki 37, ta kai daf da karshe a Europa League na bana.

Wasan da aka buga a bana tsakanin ƙungiyoyin biyu:

English League Cup ranar Alhamis 6 ga watan Fabrairu 2025

  • Liverpool 4 - 0 Tottenham

English League Cup ranar Laraba 8 ga watan Janairu 2025

  • Tottenham 1 - 0 Liverpool

Premier League ranar Lahadi 22 ga watan Disamba 2024

  • Tottenham 3 - 6 Liverpool

Tun farko Liverpool ta sa ran lashe kofi huɗu a bana, sai dai kuma an yi waje da ita a FA Cup da doke ta da Newcastle United ta yi a wasan karshe a Carabao Cup a Wembley.

Haka kuma Liverpool, wadda ta ja ragama teburin Champions League, ta yi ban kwana da gasar a zagaye na biyu a hannun Paris St Germain.

Liverpool, wadda ta buga wasa 33 a Premier League kawo yanzu ta ci karawa 24 da canjaras bakwai da rashin nasara biyu.

Haka kuma ƙungiyar Anfield ta ci ƙwallo 75, sannan aka zura mata 31 a raga a gasar ta Premier League.

Liverpool ta fara lashe Premier League a 1900/01, lokacin da ake kiran gasar Football League, kuma a kaka ta 13 da aka fara wasannin.