Za a gurfanar da mutum biyu kan lahanta idon Amarya a ranar biki a Kano

Kano

Asalin hoton, Kano police

An wallafa

Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Jihar Kano ta tabbatar da cewa za a gurfanar da wasu mutum biyu a gaban kotun majistare bisa zarginsu da yi wa idon wata amarya lahani ana tsaka da bikinta.

A karshen mako ne yayin wani biki wasu jami’an tsaron bijilanti suka yi kokarin hana kade-kaden da ake yi kasancewar an hana kidan DJ, abin da ya haifar da hatsaniyar da ta yi sanadin raunata idon amarya. 

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da afkuwar lamarin, inda ta ce ta kama mutum biyu.

Rahotanni sun ce a lokacin da ake shagalin biki sai ƴan bijilanti suka je wurin inda rikici ya kaure har aka buga wa amaryar dutse a ido.

Mijin amaryar Mustapha Bala ya ce ba za su amince da abin da aka yi mata ba.

"Gaskiya ban ji daɗi ba, don da na zo na tarar da ita cikin wani hali tana kuka gaskiya hankalina ya riga ya tashi don da na je gida kwana na yi ban yi bacci ba," in ji Mustapha.

Ya bayyana cewa duk da lamarin da ya faru duk da haka an samu zarafin ɗaura auren amma ya ce har yanzu ba a tare ba sakamakon fafutikar da suke yi ta nema mata lafiya.

Angon ya ce duk da amaryar ta samu matsala da idonta duk da haka zai zauna da ita a haka kuma ya ci gaba da soyayya da ita kamar yadda ya saba a baya.