Rivers ta ci Kano Pillars a Premier ta Najeriya

Kano Pillars

Asalin hoton, Kano Pillars

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kano Pillars ta yi rashin nasara 1-0 a gidan Rivers United a wasan mako na 15 a gasar Premier League da suka kara ranar Lahadi.

Rivers ɗin ta ci ƙwallon ta hannun Aniekeme Okon saura minti 15 su je hutu, haka suka koma zagaye na biyu zuwa tashi daga karawar da cin Pillars 1-0.

Da wannan sakamakon Pillars, wadda ake kira sai masu gida tana ta 10 ɗin teburi da maki 19, bayan cin wasa biyar da canjaras huɗu aka doke ta biyar daga ciki.

Ita kuwa Rivers tana ta ɗaya a kan teburi da maki 29, bayan karawar mako na 15.

Kano Pillars za ta karɓi bakuncin Katsina United a wasan mako na 16 ranar Lahadi 8 ga watan Disamba a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar mata.

Ita kuwa Rivers United za ta je gidan Enugu Rangers a dai ranar ta Lahadi a babbar gasar tamaula ta Najeriya.

Wasu sakamakon wasannin ranar Lahadi 1 ga watan Disamba

  • El-Kanemi Warriors 0-0 Bayelsa United
  • Rivers United 1-0 Kano Pillars
  • Ikorodu City 4-1 Akwa United
  • Katsina United 1-0 Sunshine Stars
  • Heartland 3-2 Nasarawa United
  • Niger Tornadoes 2-1 Remo Stars

Sakamakon wasannin ranar Asabar 30 ga watan Nuwamba

  • Lobi Stars 1-0 Kwara United
  • Bendel Insurance 2-1 Plateau United