Senegal ta ci wasan farko, ta kori Qatar daga Kofin Duniya

Senegal

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Senegal ce ƙasar Afirka kaɗai da ta ci wasa zuwa yanzu
An wallafa

Masu masaukin baƙi Qatar sun fice daga Gasar Kofin Duniya bayan sun yi rashin nasara a karo na biyu a hannun Senegal.

Ƙasar da ke Gabas ta Tsakiya ta yi bakin ƙoƙarinta amma ta zama tawaga ta farko da ta fice daga gasar tun a zagayen rukuni bayan Netherlands da Ecuador sun yi canjaras 1-1 a nasu wasan na Rukunin A.

A gefe guda kuma, Senegal ta kama ƙasa a rukunin da makinta uku, abin da ya sa ta zama ƙasar Afirka ta farko da ta ci wasa zuwa yanzu.

Boulaye Dia ne ya fara jefa ƙwallo a ragar masu masaukin baƙin minti huɗu kafin a tafi hutun rabin lokaci.

An sake sare gwiwar Qatar ne bayan Famara Diedhiou ya ci ƙwallo ta biyu minti uku bayan dawowa daga hutun.

Sai a minti na 78 Muntari ya farke wa Qatar ƙwallo ɗaya amma minti shida a tsakani Dieng ya ƙara ta uku, wadda ta sa masu masaukin baƙin komawa ƙasan teburin rukunin ba tare da maki ko ɗaya ba.

Senegal za ta buga wasa na gaba kuma na ƙarshe a rukuni da Ecuador ranar 29 ga watan Nuwamba.