An buɗe wuta kan masu zanga-zanga a Iran

.

Asalin hoton, twitter

An wallafa

Mutane sun fito fiye da kowane lokaci domin yin zanga-zanga tun bayan da aka fara boren nuna adawa da gwamnatin Iran, makonni shida da suka gabata.

Dubun-dubatar mutane ne suka fito kan hanyoyin manyan biranen ƙasar, da ma wasu wurare inda zanga-zangar ta lafa a baya.

Ƙazancewar zanga-zangar na zuwa ne bayan kwana 40 da rasuwar matashiya Mahsa Amini, wadda ta rasu a hannun jami'an Hisbah, lamarin da ya haifar da tashin-tashina.

Wannan ne ƙalubale mafi girma da gwamnatin musuluncin ƙasar ke fuskanta tun bayan samar da ita.

Wata hukumar kare haƙƙin ɗan'adam da ke ƙasar Norway, ta ce jami'an tsaron Iran sun hallaka masu zanga-zanga aƙalla 234, cikin su har da yara 29.

Gwamnatin ƙasar ta bayyana cewa ƙasashen yamma ne suka kitsa zanga-zangar.

Bidiyoyin da aka wallafa a ashafukan sada zumunta, waɗanda BBC ta tabbatar da sahihancin su, sun nuna tururuwan mutane suna zanga-zanga a daren alhamis.

An rinƙa kunna wuta a kan titunan Tehran, babban birnin ƙasar, yayin da wasu ke furta kalaman tir a kan 'ɗan kama-karya' - suna nufin jagoran addini na ƙasar.

Hakan na zuwa ne kwana guda bayan da rahotanni suka ce ƴan sanda sun buɗe wuta kan masu zanga-zanga a birnin Saqqez, inda Mahsa Amin ke zaune kafin rasuwarta.

Wata ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta ce jami'an tsaro sun buɗe wuta kai-tsaye a kan masu zanga-zanga, kuma har yanzu ba a tantance yawan mutanen da suka mutu ba.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X

Zanga-zanga ta karaɗe ƙasar Iran ne bayan mutuwar Mahsa Amin, mai shekara 22, a ranar 16 ga watan Satumba.

Wasu rahotanni sun ce jami'an tsaro sun buge ta da kulki a kai, tare da gwara kanta a jikin mota kafin mutuwar tata.

An dai haramta wa BBC da wasu kafafen yaɗa labaru masu zaman kansu ɗauko rahoton abin da ke faruwa a Iran ɗin.

Kuma hukumomi na yin karan-tsaye ga intanet a ƙasar, abin da ke kawo cikas ga yunƙurin masu zanga-zanga na wallafa abubuwan da ke faruwa a shafukan sada zumunta.