Ko za a iya soke sakamakon zaɓen Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
Jam'iyyun adawa a babban zaben Najeriya da aka fafata a kai za su yi kokarin yin abin da za a iya cewa bai taba yiwuwa ba - shi ne samun wata kotu ta soke sakamakon zaben shugaban kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka.
Peter Obi da Atiku Abubakar an takarar da suka zo na biyu da na uku a zaben sun lashi takobin zuwa kotu domin kalubalantar zaben da aka yi yi wa Bola Tinubu na jam'iyya mai mulki ta APC wanda ya sami kashi 37 cikin 100 na dukkan kuri'un da aka kada.
Sai dai wace hujja suke da ita, kuma suna iya sa a soke wannan sakamakon zaben kuwa?
Wane lokaci jam'iyyun siyasa ke da shi na shigar da kara?
Tilas a shigar da kararrakin zabe a Najeriya cikin kwanaki 21 bayan da aka sanar da sakamakon zaben, in ba haka ba, kotuna za su yi watsi da su.
Saboda haka Peter Obi da Atiku Abubakar na da daga yanzu zuwa ranar 31 ga watan Maris ke nan.
Sai dai wannan jan aiki ne ganin cewa sai 'yan takarar sun tattaro bayanai da shaidu daga mazabu fiye da 176,000 da kuma cibiyoyin tattara bayanai fiye da 8,000 na wuraren da aka kada kuri'u da tattara sakamakon a fadin Najeriya cikin wadannan takaitattun kwanakin.
Wane lokaci kotu ke dauka kafin a bayyana hukunci?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An samar da kwanaki 180 bayan an shigar da kara ga kotunan da ke sauraren kararrakin zabe, kuma ganin cewa Mista Obi da Alhaji Abubakar kowannensu zai shigar da tasa karar ce daban da ta daya dan adawar, daga karshe kowannensu zai sami nasa hukuncin ne a lokacin da kotun da ya tunkara ta kammala sauraren kararsa.
Sai dai idan 'yan takarar biytu ba su gamsu da hukuncin da kotunan sauraren karar zaben suka yanke ba, suna iya daukaka kara zuwa kotun kolin kasar.
Daukaka karar na iya kai tsawon kwanaki 60, saboda haka za a aiya kammala shari'ar cikin watanni takwas ke nan.
Ko shari'ar na iya shafar rantsar da sabon shugaban kasa?
A'a.
Zai yi wahala kotun sauraren karar zaben ta yanke hukunci kafin ranar 29 ga watan Mayu - lokacin da za a yi bikin rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasa.
Kuma ko da kotun ta umarci a sake yin zaben, ko kuma ta bayyana wani dan takarar na daban a matsayin wanda ya lashe zaben, babu shakka sabon shugaban zai daukaka kara zuwa kotun kolin Najeriya.
Me doka ta ce game da aika wa da sakamakon zabe?
Da 'yan jarida suka matsa wa Mista Peter Obi ya bayyana hujjojin da yake da su da yace shi ne ya lashe zaben, sai ya ki cewa komai, inda shi kuma Atiku Abubakar sai ya sanar cewa ba a bi ka'ida ba kan "hanyoyin da aka bi da sakamakon da aka samar" da sakamakon zaben.
Sai dai a bayyane take cewa dukkan jam'iyyun adawar biyu za su fi mayar da hankulansu ne ga gazawar da hukumar zaben kasar ta yi na tura sakamakon zaben nan take daga rumfunan zaben kasar.
Hukumar zaben Najeriya INEC, ta ce cunkoso mai yawa aka samu, shi yasa ba ta iya wallafa sakamakon zaben a shafinta na intanet yayin da ake sanar da su a rumfunan zabe kai tsaye ba.
Kusan mako guda bayan kammala wannan zaben, akwai kimanin kashi 12 cikin 100 na sakamakon zaben da har yanzu ba a wallafa a shafin da INEC din ta samar ba.
Wani babban lauya mai suna Yemi Candide Johnson ya shaida wa BBC cewa tsare-tsaren da hukumar zaben ta saka ba daidai suke da dokar kasa ba, saboda haka za a iya soke zaben ne kawai idan ya taka dokar zaben kasar sosai.
"Idan rashin bin ka'idojin hukumar ba zai shafi sakamakon zabe ba, kasancea haka ba zai sa a a soke zaben ba. Idan wasu sakamakon zaben a wasu wuraren ba su zama daidai ba, ana iya sake yin wani zaben a wuraren, amma sai idan yin hakan na da tasiri ga ainihin sakamakon."
Wace hujja ya kamata su bayar?
A karkashin dokar zabe ta Najeriya, wanda ya shigar da kara a kotu na da aikin tabbatar wa kotun cewa ba a bi ka'idar da dokar zaben ta shimfida ba, kuma yin haka ya shafi sakamakon ta yadda zai iya sauya wanda ya lashe zaben.
Wannan na nufin sai an sami masu yin magudin zabe a yawancin rumfunan zaben Najeriya ke nan.
Bambancin kuri'u tsakanin Tinubu da Atiku ya kai kusa da kuri'a miliyan biyu, inda tsakanin Atikun da Obi kuwa akwai tazarar wasu kuri'u 700,000.
Anya 'yan adawa za su iya samun nasara a kotu kuwa?
Duk da cewa ba a taba soke zaben shugaban kasa ba a Najeriya, amma an sha soke zabuka a wasu matakan.
Kuma Mista Obi na cikin wadanda suka ci gajiyar soke wasu zabukan.
Sai da ya shafe shekara uku yana jira kafin ya sami kama aiki a matsayin zababben gwamna a 2006 bayan da ya yi nasarar gamsar da shari'a cewa shi ne ya lashe zaben jihar Anambra na 2003.
Ya iya gamsar da kotun zabe ta musamman da ta daukaka kara cewa shi ne ya sami kuri'u mafi yawa a zaben gwamnan kuma a karshe aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.











