Yaƙin Ukraine: Sojojin Rasha na ja-in-ja kan adadin mace-macen yaƙi

Asalin hoton, Reuters
Takardun sirrin Amurka da aka kwarmata sun bankaɗa yadda ɓangarorin dakarun tsaron Rasha suka samu rashin jituwa, lamarin da ya sa har aka zargi ma'aikatar tsaro da rage yawan mutanen da suka mutu lokacin yaƙi a Yukren.
Rasha dai, ba ta cika magana a bainar jama'a game da yawan mace-macen dakarunta a fagen yaƙi ba.
Sai dai takardun sirrin sun nuna jami'an tsaron leƙen asirin Rasha FSB na iƙirarin cewa hukumomi ba sa haɗa ƙirge da mace-macen Dakarun Tsaron Ƙasa na Rasha da sojojin haya na Wagner da kuma wasu.
Rasha dai tuni ta yi gargaɗin cewa bayanan da aka kwarmata ɗin mai yiwuwa na jabu ne, kuma da gangan Amurka ta yasar da su.
Sai dai, bayanan sun tabbatar da abubuwan da tun tuni aka sani: cewa sojojin Rasha da hukumomin tsaro sun yi ta samun saɓani game da yadda ake tafiyar da yaƙin na Yukren.
Rasha kuma ta yi ta gujewa faɗar adadin dakarunta da suka mutu ko suka jikkata a bainar jama'a.
Lissafin hukumar leƙen asiri ta FSB da aka ba da bayani game da mutuwar kusan 110,000 a watan Fabrairu ya yi matuƙar gaza adadin wannan mako da aka samu kwanan baya a takardun Amurka da aka kwarmata.
Takardun dai sun ƙiyasta cewa Rasha ta yi asarar mutane tsakanin 189,500 zuwa 223,000, yayin da mutum 35,500-43,000 suka mutu a fagen daga.
An fitar da alƙaluman Rasha na baya-baya ne a hukumance a watan Satumban bara, lokacin da ta tabbatar da mutuwar soja 5,937.
Irin waɗannan takardu da aka kwarmata sun ce rage yawan mutanen da aka kashe ko aka jikkata a tsarin tafi da harkoki na nuna "ci gaba da ƙiyawar" sojoji wajen kai labarai marasa daɗi ga manyan jagororin soji.
Sau da yawa, masharhanta kan nuna cewa, ana kange Shugaba Vladimir Putin daga sanin haƙiƙanin asarar da Rasha ke tafkawa a fagen daga, kuma wannan ƙiyasi, ga alama ana samo shi ne ta hanyar kutse cikin layukan sadarwa.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wata takardar bayanan asirin wadda aka yi wa tambari da babban sirri, ta yi bayani a kan wasu "bayanan yaƙi" tsakanin ma'aikatar tsaro da kuma shugaban kamfanin sojojin haya na Wagner, Yevgeny Prigozhin a watan Fabrairu.
Prigozhin ya sha zargin sojoji da dakatar da safarar makamai, yayin da dakarunsa ke fafatawa don ƙwace birnin Bakhmut na gabashin Yukren.
Bayanan kwarmaton sun kuma ambato jami'an ma'aikatar, na nuna cewa suna neman "abokan ƙawancen da za su yi faɗa da dakarun Prigozhin maimakon yin hakan, su da kansu".
Babban abin bankaɗar dai, shi ne bin diddigin da aka yi na takardun sirrin ya tabbatar da cewa gagarumar asarar da Dakarun Tsaro na Ƙasa ko Rosgvardia suka yi "mai yiwuwa zai daƙile ƙoƙarin hukumomin Moscow wajen tsare dukkan yankunan da Rasha ta mamaye kuma ta haɗe da ƙasarta".
Dakarun rundunar Rosgvardia sun shiga cikin yaƙin kuma sun taimaka wajen shirya ƙuri'un raba gardama da Rasha ta yi maguɗi, wadanda suka sa Putin ya haɗe yankunan Yukren huɗu da ƙasarsa a watan Satumban da ya wuce.
Abin da aka sani game da mutumin da ya kwarmata bayanan sirrin ƙalilan ne, sai dai jaridar Washinton Post ta ruwaito cewa wani ɗan bindiga ɗaɗi ne lokacin da yake cikin shekarunsa na ashirin, sa'ar da yake aiki a wani sansanin sojojin Amurka.
A cewar Washington Post, mai kwarmaton ya saurari bayanai sannan ya rubuta su kafin daga bisani, ya buga abin da ya gani ƙunshe a takardun sirrin cikin sansanin sojojin, daga nan kuma ya wallafa hotunan takardun.
Cikin hotunan takardun da aka wallafa, akwai ɗaya da ke nuna ƙididdigar da Amurka ta yi wa "yaƙin ƙare-ƙarfi da ba a san ƙarshensa ba" na Rasha a lardin Donbas na gabashin Yukren.
Inda ta ce matuƙar ba wata "farfaɗowar bazata" dakarun Rasha suka yi ba, Yukren za ta iya kassara manufofin Rasha na shiga wannan yaƙi, "abin da zai zama sanadin yaƙin lokaci mai tsawo har gaban shekara ta 2023".
Mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Sergei Ryabkov ya nuna cewa mai yiwuwa da gangan Amurka ta fito da takardun bayanan.
A matsayinta na wani "ɓangare a yaƙin", ya ce gwamnatin Washington mai yiwuwa tana neman hanyar da za ta "rufta abokan gaba wato Tarayyar Rasha".











