Afcon 2023: Yadda tawaga takwas ta kai kwata fainals a Ivory Coast

Afcon 2023

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

An kammala wasannin zagaye na biyu ranar Talata a gasar cin kofin Afirka da Ivory Coast ke karbar bakunci, za a fada zagayen quarter fainals.

An samu tawaga takwas da za ta ci gaba a zagayen daf da na kusa da na karshe da ya kunshi Angola da Najeriya da Guinea da Jamhuriyar Congo.

Sauran sun hada da Cape Verde da Ivory Coast da Afirka ta kudu da kuma Mali

Wasa takwas aka buga a zagaye na biyu da ta kai an samu tawaga takwas da za ta kara a zagaye na uku wato na quarter finals da za a fara daga ranar Juma’a.

An zura kwallo 16 a raga da jan kati biyar da kuma katin gargadi 31, wato mai ruwan dorawa da aka raba.

Angola ce ta fara samun tikitin kuma karo na uku da ta kai wannan matakin a gasar da ta ke yi karo na takwas jimilla.

Angola ta yi nasarar doke Namibia 3-0 a zagaye na biyu ranar Asabar.

Afcon 2023

Asalin hoton, Getty Images

Super Eagles ce ta biyu da ta kai zagayen quater finals, bayan doke Indomitable Lions a wasan hamayya ranar Asabar da ci 2-0.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Nigeria mai buga Afcon karo na 20 ta samu gurbin daf da na kusa da na karshe karo na 17, bayan da ta lashe kofin a 1980 da 1994 da kuma 2013.

Wannan shi ne karo na bakwai da Guinea za ta fafata a quarter finals a karo na 14 da take halartar wasannin.

Guinea wacce ta fara halartar Afcon 1970 ta taba yin ta biyu 1976, shi ne kwazo mafi girma da ta taka a tarihin wasannin.

Ranar Lahadi Guinea ta yi nasara a kan Equatorial Guinea da ci 1-0.

Jamhuriyar Congo ce ta hudu da ta samu zuwa matakin quarter finals a bana kuma karo na 11, bayan da ta dauki kofin a 1968 da kuma 1974.

DR Congo ta tashi 1-1 da Masar a karawar zagaye na biyu, sannan aka yi karin lokaci da zuwa bugun daga kai sai mai tsaron raga.

A bugun na fenariri ne Jamhuriyar Congo ta ci 8-7, karon farko da ta yi nasara a kan Masar a wwasa bakwai baya da suka fafata.

Wannan shi ne wasan quarter finals na biyu da Cape Verde za ta fafata, wadda ke buga Afcon karo na hudu.

Wacce ta fara halartar gasar kofin Afirka a 2013 ta kai matakin ƴan takwas a shekarar da kuma wanda za ta fafata a Ivory Coast.

Ranar Litinin mai masaukin baki, Ivory Coast ta kai zagayen daf da na kusa da na karshe, bayan da ta fitar da Senegal mai rike da kofin a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Afcon 2023

Asalin hoton, Getty Images

Ivory Coast mai kofin Afcon biyu da ta lashe a 1992 da kuma 2015 za ta buga quarter finals karo na 14, bayan da take karawa a gasa ta 25.

Tun farko da kyar da gumin goshi Ivory Coast ta kai zagaye na biyu, bayan da ta yi ta uku a rukunin farko da maki uku.

Mali ce ta bakwai da ta samu gurbin shiga zagayen ƴan takwas, bayan da ta yi nasara a kan maƙwanciyarta Burkina Faso ranar Talata.

Karo na bakwai kenan da Mali za ta buga zagayen daf da na kusa da na karshe, wadda ta yi rashin nasara a wasan karshe a 1972 da Congo Dr ta zama zakara.

Afirka ta Kudu ce ta samu gurbin karshe na takwas da za ta fafata a zagaye na uku a gasar Afcon da Ivory Coast ke karbar bakuncin.

Ranar Talata Afirka ta Kudu ta yi nasara a kan Morocco da ci 2-0 a wasan zagaye na biyu.

Tun farko an dauka cewar Atlas Lions ce za ta kai zagaye na ukun, bayan da ta yi abin kirki a gasar kofin duniya a Qatar a 2022, wadda ta kai gurbin daf da karshe.

Morocco ce ta daya daga Afirka da ta kai wannan matakin a babbar gasar tamaula ta duniya.

Wasannin daf da na kusa da na karshe

Ranar Juma'a 2 ga watan Fabrairun 2024

  • Nigeria da Angola
  • Jamhuriyar Congo da Guinea

Ranar Asabar 3 ga watan Fabrairun 2024

  • Mali da Ivory Coast
  • Cape Verde da South Africa