Hotunan Afirka na mako daga 12 zuwa 18 ga watan Agustan 2022

An wallafa

Zababbun hotuna daga sassan Afirka na wannan makon:

.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani mutum ke nan a lokacin da yake kokarin taimakon wata mata ana tsaka da addu'oi a cocin Legio Maria ranar Lahadi a Kisumu da ke Kenya...
Washegari kuma, masu ibada a cocin na Legio Mary, wani reshe na mabiya darikar katolika, sun gudanar da taron addu'oi da ake shafe dare ana yi duk shekara a Kisumu.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Washegari kuma, masu ibada a cocin na Legio Mary, wani reshe na mabiya darikar Katolika, sun gudanar da taron addu'oi da ake shafe dare ana yi duk shekara a Kisumu.
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Juma'a an samu karin bukukuwa da suka shafi addini a Osogbo da ke Najeriya yayin da wata Ba'amurkiya ta tsaya domin yin hoto a bikin Osun Osogbo inda mabiya addinin gargajiya na Yarabawa suke ibada a wani tsarkakakken waje da ya kasance cikin wanda Unesco ta sanya a wuraren tarihi.
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An nada Ndavi Nokeri a matsayin sarauniyar kyau a Afirka ta Kudu a wani kasaitaccen bikin karramawa da aka yi a Pretoria...
Lalela Mswane ke nan, wadda ta rasa kambunta na mace mafi kyau a Afirka ta Kudu, yayin da take daukar hoto a bikin...

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Lalela Mswane ke nan, wadda ta rasa kambunta na sarauniyar kyau a Afirka ta Kudu, yayin da take daukar hoto a bikin...
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani matashi a kan doki a wurin wani juyayin tunawa da kisan kiyashin da aka yi a Marikana lokacin da wasu masu hako ma'adanai 34 suka mutu sakamakon yajin aiki kan albashi shekara 10 da suka gabata.
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A can Mutoto da ke Uganda, hoton wani matashi ne yayin wani taron gargajiya kan kaciya da ake kira Imbalu wanda ake shiryawa matasa maza da suka girma a yankin Bagisu...
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani matashi ke nan dan shekara 15 a wajen bikin tsaye yana daukar hoto.
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani matashi zaune a gaban wuta a Nairobi da ke Kenya yayin da magoya bayan Jam'iyyar Azimio la Umoja- One Kenya ke zanga-zanga bayan da hukumomi suka sanar da William Ruto a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa inda abokin hammayarsa Raila Odinga ya sha kaye...
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An ci gaba da samun tashin hankali dai-dai lokacin da wani jami'in dan sanda ya harba wa masu zanga-zangar hayaki mai sa hawaye a Kisumu...
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sai dai akwai masu murna... yayin da magoya bayan Ruto a birnin Nakuru ke ta farin cikin nasararsa.
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A Masar kuma wani mutum ne yake amfani da dutsen guga na gargajiya a shagonsa.
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A Turkiyya, Yar dambe, Belouarrat Oumaima daga Morocco na gwada kwanji da Hayriye Hancer Turksoy yar kasar Turkiyya ranar Laraba a gasar Islamic Solidarity Games karo ta biyar...
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A dai gasar, dan Senegal Gaye Serigne Amsatou na barje gumi da Mohammadreza Sedighi daga Iran a kokawar Judo.
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A fannin nishadi kuma, wata mawakiya Eno Williams 'yar Birtaniya daga Najeriya ce ke nishadantar da masu kallo tare da takwaranta na Ghana Alfred Kari Bannerman a Winchester da ke Ingila a bikin Boomtown.
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Yadda shugaban gamayyar kungiyar UFDD Mahamat Nouri ya samu tarba daga yan uwa da magoya baya a filin jirgin sama bayan shafe shekara 16 yana gudun hijra.Komawarsa N'Djamena da ke Chad gabanin muhimmiyar tattaunawa kangudanar da zabe, bayan fiye da shekara daya bayan mulkin sojoji.