Yadda sauyin kuɗi ya bar baya da ƙura a 2023

Asalin hoton, Getty images
- Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
- An wallafa
Shekara ɗaya tun bayan da babban bankin Najeriya CBN ya sanar da sauya fasalin takardun naira, har yanzu ƴan Najeriya suna fuskantar ƙarancin kuɗi.
Wani abu da zai yi wuya al'ummar Najeriya su manta da shi, shi ne yadda a farko-farkon aiwatar da tsarin ta kai ga mutane na sayen naira kamar yadda ake siyan kuɗaɗen ƙasashen waje.
Ga kuma yadda aka fuskanci rashin kuɗi a na'urorin cirar kuɗi da kuma wuraren masu na'urar POS.
Akwai lokutan da bankuna da masu motocin haya da sauran ƴan kasuwa suke ƙin karɓar tsofaffin takardun kuɗin duk da umarnin a ci gaba da amfani da su.
Bari mu duba irin taƙaddamar da aka yi ta yi game da batun sauya takardun kuɗin da har yanzu za a iya cewa ba ta sauya zani ba.
Ƙarawa da janye wa'adin amfani da tsofaffun takardun kuɗi
Babban Bankin Najeriya, CBN tun a 2022, ya bayyana cewa a ƙarshen watan Janairu ne za a daina amfani da tsofaffin takardun naira 200 da 500 da kuma 1000 sai dai ci gaba da fuskantar ƙarancin takardun kuɗin ya sa aka gaza tafiya kan wa'adin inda bankin ya sake tsawaita wa'adin zuwa 10 ga wa Fabarairu.
Sai dai kafin zuwan lokacin ne wasu gwamnonin jihohin arewacin Najeriya uku - Zamfara da Kogi da Kaduna suka maka gwamnatin tarayya gaban Kotun Ƙoli saboda abin da suka kira matsananciyar wahalar da al'ummarsu ke sha sanadiyyar tsarin na gwamnati. Ƴan kwanaki bayan nan ne, kotun ta bai wa gwamnati umarnin ta janye ƙudirin daina amfani da tsofaffin takardun kuɗin inda ta buƙaci a ci gaba da amfani da tsoffafi da kuma sababbin takardun kuɗin har zuwa ƙarshen Disamba.
Hakan ta faru bayan da aka samu ƙarin wasu jihohi a jumulla 16 da suka soki tsarin sabunta takardun kuɗin na gwamnati.
Bayan nan kuma, an yi ta samun umarni daga tsohuwar gwamnati waɗanda suka ci karo da umarnin kotu. An ci gaba da shan wahala saboda ƙarancin takardun kudin har zuwa lokacin da ƴan Najeriya suka yi zaɓe ranar 25 ga watan Fabarairu wanda kafin nan, wasu na shakkun da wuya a iya gudanar da zaɓe a ranar da aka tsara.
Boren NLC da tsawaita harkokin banki zuwa ranakun ƙarshen mako
Bayan babban zaɓen shugaban ƙasa, ƙungiyar ƙwadago NLC ta yi barazanar shiga yajin aiki na gama-gari a watan Maris domin nuna fushinta kan yadda ƴan Najeriya ke ganin tasku kafin su samu takardar naira a hannunsu, ga kuma matsalar da janye tallafin mai ta haifar. Sai dai ƙungiyar ta janye ƙudirinta ƴan kwanaki kafin ranar.
Ta ce ta yi haka ne saboda zaman da suka yi da gwamnati wadda ta yi alƙawarin samar wa al'umma sauƙi abin da ya sa NLC ta sha alwashin cewa matuƙar mutane suka ci gaba da fuskantar wahala wajen samun takardun kuɗi, za ta shiga yajin aiki.
Daga cikin alƙawuran da gwamnati ta yi akwai samar da yalwar takardun kuɗin ta yadda mutane za su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum ba tare da fuskantar wata matsala ba.
Wannan ya sa CBN ya bai wa bankunan kasuwanci umarnin buɗewa a ranakun ƙarshen mako domin tabbatar da cewa mutane sun samu garin kuɗi a hannunsu.
A ina aka kwana?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Harkokin kasuwanci sun shiga wani yanayi ta dalilin ƙarancin kuɗin musamman a ɓangaren ƙananan ƴan kasuwa.
Kotun ƙoli a ranar 29 ga watan Nuwamba ta ce a ci gaba da amfani da kuɗaɗen har illa ma sha Allahu bayan ta amince da buƙatar ministan shari'a na ƙasa ta yin hakan.
Daga bisani shi ma babban bankin ƙasar ya fitar da sanarwar da ta nuna a ɗore da amfani da sababbi da tsofaffin kuɗaɗen.
Sai dai wannan umarni ya bar baya da ƙura kasancewar har yanzu mutane na shan wahala wajen samun takardun kuɗi a hannunsu domin tafiyar da bukukuwan ƙarshen shekara.
Ƙwararru a fannin tattalin arziki sun rabu kan tsarin - wasu na ganin shi ne tsari mafi muni da aka taba yi a Najeriya tun bijiro da shirin SAP a shekarar 1986 yayin da wasu ƙwarrarun kuma suke ganin tsarin abu ne mai kyau da zai ciyar da Najeriya gaba musamman idan aka ce an yi wa tsarin cikakken nazarin da ya kamata.
Abin da ƴan Najeriya a yanzu suke dako shi ne ko za ta sauya zani a wahalhalun da suke sha wajen samun garin kuɗi a hannunsu cikin sauƙi musamman a sabuwar shekara?










