Abin da ya sa Kotun Kolin Kenya ta tabbatar da zaben Ruto ta yi watsi da karar Odinga

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Magoya bayan Mr Ruto sun fantsama kan tituna domin yin murna
An wallafa

Kotun Kolin Kenya ta tabbatar da cewa an bi sahihiyar hanya wajen zaben William Ruto a matsayin shugaban kasar, kuma ta yi watsi da kararrakin da aka shigar da zummar soke zaben da aka yi ranar 9 ga watan Agusta.

Abokin hamayyarsa, Raila Odinga, da mutane da dama sun yi zargin cewa an yi gagarumin magudi, ciki har da lalata fom din rubuta sakamakon zabe.

Mr Ruto ya yi nasara da kashi 50.5 na kuri'un da aka kada. A makon gobe ne za a rantsar da mataimakin shugaban, mai shekara 55, a matsayin shugaban Kenya na biyar.

An yi fatali da kararraki takwas da ke kalubalantar zaben. Kotun Kolin ta gano cewa wasu daga cikin kararrakin an shigar da su ne bisa takardun bogi.

Alkaliyar Alkalai Martha Koome a matakin da dukkan alkalai bakwai suka amince da shi, sun yi watsi da karar.

Ta ce babu wata gamsasshiyar shaida da ke nuna cewa an lalata tsarin zabe na intanet kamar yadda aka yi zargi.

Ms Koome ta ce Mr Ruto ya cika dukkan sharudan kundin tsarin mulki wajen samun kashi 50+1 na kuri'un da aka kada.

Hukuncin ya kawo karshen rikicin zaben da aka soma a watan jiya.

Tawagar Mr Odinga ta yi amfani da matsayin hudu daga cikin kwamishinonin hukumar zabe bakwai - wadanda suka ki amincewa da sakamakon da shugaban hukumar zaben ya sanar - domin shigar da karar.

Amma kotun, a yayin da take magana kan "rashin tsarin" hukumar zaben na gudanar da harkokin cikin gidanta, ta ce ba ta gamsu da ikirarin da ke cewa ya kamata a soke zaben kawai domin shugaban hukumar zaben ya yi gaban kansa wajen sanar da sakamako.

"Shin ya dace mu soke sakamakon zabe saboda tirka-tirkar da wasu suka yi a karshen zaben wadda babu cikakken bayani a kanta?", kamar yadda alkaliyar ta tambaya.