Raila Odinga ya yi watsi da sakamakon zaben Kenya

Asalin hoton, AFP
Dan takarar jam’iyyar hamayya a Kenya, Raila Odinga, ya yi watsi da sakamakon zaben da ya bai wa abokin hamayyarsa William Ruto, nasara.
A wani taron manema labarai, ya bayyana sakamakon da aka bayyana a jiya Litinin a matsayin wanda ya haramta tare da alwashi kalubalantar nasarar Mista Ruto, a kotu.
Mista Odinga ya caccaki shugaban hukumar zaben kasar, Wafula Chebukati, kan sanar da sakamakon duk da cewa malaman zabe da dama na korafin cewa an tafka kura-kurai a wajen kidaya kuri’u.
Mista Ruto ya yi nasara a wannan zabe ne bayan lashe sama da kashi 50.9 cikin 100 na kuri’un da aka kada – wanda hakan ya datse kofar tafiya zaye na biyu.
Kungiyoyin da suka sa ido kan zaben sun tabbatar da sahihancinsa.
Wannan ne karo na biyar da Odinga mai shekara 77 ya tsaya takarar shugaban ƙasar. Ya ƙalualanci sakamakon zaɓuka biyu da suka gabata, ciki har da wanda kotu ta yarda aka sake zaɓen na shekarar 2017.
A wannan karon, shugaban hukumar zaɓen Wafula Chebukat ya ce Odinga ya samu kashi 48.8 cikin 100 a zaɓen wannan karon inda shi kuma Mista William Ruto ya samu kashi 50.5 cikin 100.
Mista Odinga ya zargi Mista Chebukati da yin maguɗi yana mai cewazai shigar da ƙara.
Ya ce Mr Chebukati ya karya dokar sanar da sakamakon ba tare da samun goyon bayan kwamishinonin huku,mar zaɓen ba.
Wannan wani abu ne da wataƙila sai an garzaya zuwa kotu.
Mintuna kaɗan kafin Mista Odinga ya yi jawabi, huɗu daga cikin kwamishinonin hukumar zaɓen bakwai da suka ƙi amincewa da sakamakon zaɓen sun yi wani taron manema labarai don faɗar dalilansu..
Sun zargi Mr Chebukati da mayar da su saniyar ware a wajen sanar da sakamakon da suka ce "lissafinsa yana cike da kura-kurai."
End of Wasu labaran da za ku so ku karanta
Mataimakiyar shugaban hukumar zaben Juliana Cherera ta ce idan aka tara jumullar kason yawan ƙuri'un da shugaban hukumar zaɓen ya sanar, zai zama kashi 100.01%.
Amma tawagar binciken ƙwaf ta BBC ta ce kuskure ne aka samu ba wai abu ne da aka yi da gangan ba.
Sai dai duk da haka Mista Odinga ya yaba wa kwamishinonin huɗu kan "gwarzantakarsu".
"Muna alfahari da waɗanda suka dage suka tsaya akan gaskiyarsu kan abin da Mr Chebukati ya yi duk da buɗe musu ido da aka yi amma ba su ji tsoron komai ba, ƴan Kenya na tare da su," in ji shi.











