Man United ta buga kurman duro karon farko karkashin Ten Hag

Erik tten Hag

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Manchester United ta tashi 0-0 a wasan mako na 11 a gasar Premier da suka kara a Old Trafford ranar Lahadi.

Kungiyoyin sun samu damar makin zura kwallo a raga tun farko, musamman Newcatle da kwallo biyu ya bugi turke.

Marcus Rashford ya samu dama mai kyau a karshen lokaci, wanda ya sawa kwallo kai ta yi fadi ta fita waje.

Karon farko da sabon koci, Erik ten Hag ya tashi 0-0 a dukkan wasan da ya ja ragamar United kawo yanzu a bana.

Kociyan ya ja ragamar wasa 13 a dukkan fafatawar da United ke yi a kakar 2022/23 kawo yanzu.

Cristiano Ronaldo ya buga wasan, wanda daga baya Rashford ya canja, an kuma ga kyaftin din Portugal na jijjiga kai a lokacin da zai fita daga filin.

Da wannan sakamakon Manchester United wadda ta yi wasa tara tana da maki 16, ita kuwa Newcastle tana da 15 biye da kungiyar Old Trafford.

Ranar Laraba 19 ga watan Okboba, Manchester United za ta karbi bakuncin Tottenham a wasan da zai yi zafi.

A kuma ranar Newcastle United za ta yi wa Everton masauki a St Jamrs Park.