'Yadda ni da ƴaƴana muka riƙa tsallake gawarwaki kan hanyar neman tsira a Gaza'

Asalin hoton, Jehad El-Mashhrawi
Bayan Isra'ila ta kwashe makonni ta na luguden wuta, a ranar 16 ga Nuwamba Jehad El-Mashhrawi da iyalinsa sun tsere daga gidansu a arewacin Gaza. Mai daukar hoton na Sashen Larabci na BBC ya ba da labari mai ban mamaki da al'ajabi game da abin da shi da matarsa da 'ya'yansa suka fuskanta yayin da suke kan hanyar zuwa kudanci.
Gargaɗi: Wannan labarin ya ƙunshi hotuna da ka iya tayar da hankali
A gurguje muka fita. Muna tsakiyar gasa burodi sai mu ka yi la'akari da cewa bam na faɗawa gidajen makwabtanmu, ɗaya bayan ɗaya. Na san nan ba da jimawa ba abin zai iso kan mu. Mun shirya wasu jakunkuna wai ko da hakan ya faru, amma cikin gaggawa mun manta da su. Ba mu ma rufe ƙofar gidan ba.
Mun jinkirta tafiyarmu don ba ma so mu ƙaura da iyayena tsofaffi kuma mun ɗauki shekaru muna tanadi don gina gidanmu a al-Zeitoun, amma a ƙarshe dole ne mu yi hijira. Ɗana, Omar, ya mutu a watan Nuwamban 2012, yayin wani yaƙin da Isra'ila kuma ba zan iya yin kasadar rasa wasu yaran ba.
Na san cewa babu wutar lantarki a kudanci ƙasa, babu ruwan sha kuma sai mutane sun yi layi na sa'o'i don amfani da banɗaki. Amma a ƙarshe, mun ɗauki kwalbar ruwa da ragowar burodi, mun haɗu da dubban wasu da ke tafiya mai haɗari ta hanyar Salah al-Din zuwa kudanci, inda Isra'ila ta ce akwai tsaro.

Asalin hoton, Majed Hamdan/Associated Press
Akasrin daginmu sun yi tafiya tare - matata Ahlam, da ’ya’yanmu maza huɗu, ‘yan shekara biyu, takwas, tara da 14, iyayena da ’yan’uwana maza da mata da ’ya’yansu.
Hanyar Salah al-Din
Mun yi tafiya na sa’o’i kuma mun san cewa a ƙarshe za mu bi ta wani shingen binciken kan hanya da Isra’ila ta kafa a lokacin yaƙin. Mun kasance a firgice, yarana suna tambaya: "Menene sojojin za su yi mana?"
Mun tsaya kusan kilomita daya daga shingen binciken kuma muka haɗu da wani dogon jerin mutane waɗanda suka cika titin gaba ɗaya. Mun kwashe sama da sa'o'i hudu muna jira kuma mahaifina ya suma sau uku.
Akwai sojojin Isra'ila suna kallonmu daga gine-ginen da bama-bamai suka ruguza a gefe ɗaya na titin da kuma wani fili da babu kowa a ɗaya bangaren.
Yayin da muka matso kusa da shingen binciken, sai muka ga ƙarin sojoji a sama wani tudu a cikin wani tanti. Muna tsammanin su ne ke gudanar da shingen binciken daga can nesa, suna kallon mu ta abin hangen nesa kuma suna amfani da lasifika don gaya mana abin da za mu yi.
Akwai buɗaɗɗun kwantena guda biyu kusa da tantin. Maza na bi ta cikin ɗaya, mata kuma na bi ta ɗayan, ga kyamarori suna kallon mu a koda yaushe. Lokacin da muka wuce, sojojin Isra'ila sun nemi mu nuna katin shaidarmu kuma an ɗauke mu hoto.
Ya kasance kamar ranar tashin ƙiyama.

Asalin hoton, Maxar
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Na ga an tsare mutane kusan 50, dukansu maza, ciki har da biyu daga cikin makwabtana. An dakatar da wani matashi saboda ya rasa takardunsa kuma ya kasa tunawa lambar takardar shaidarsa. Wani mutumin da ke kusa da ni a kan layi, wani sojan Isra’ila ya kira shi da ɗan ta’adda, kafin daga na ya tafi da shi.
An ce su tuɓe rigunansu su zauna a ƙasa. Daga baya aka ce wasu su mai da kayansu su tafi, wasu kuma an rufe masu ido.
Na ga wasu fursunoni huɗu da aka rufewa idanu, ciki har da makwabtana, an kai su bayan wani tudun yashi a kusa da wani gini da ya ruguje. Bayan mun daina ganinsu, sai muka ji ƙarar harbin bindiga. Ba ni da masaniya ko an harbe su ko a'a.
Wani abokin aikina a Alkahira ya tuntuɓi sauran mutanen da suka yi tafiya irin tawa. Ɗaya daga cikinsu mai suna Kamal Aljojo ya ce bayan da ya bi ta shingen binciken mako guda kafin isar mu, ya ga gawawwaki, amma bai san yadda suka mutu ba.
Abokin aikina ya kuma yi magana da wani mutum mai suna Muhammed wanda ya bi ta shingen bincike a ranar 13 ga Nuwamba. Muhammed ya shaida wa BBC cewa "wani soja ya ce in cire duka tufafina, har da kamfai." Ya ƙara da cewa: "Na kasance tsirara a gaban duk wanɗanda ke wucewa. Na ji matuƙar kunya. Haka nan kawai wata Soja ta nuna min bindigar ta ta yi dariya kafin ta yi sauri ta ɗauke ta, an wulakanta ni." Muhammed ya ce sai da ya jira tsirara na tsawon sa'o'i biyu kafin aka bar shi ya tafi.
Ko da yake ni da matata da ’ya’yana da iyayena mun wuce shingen binciken lafiya, sai da aka tsare ’yan’uwana biyu.
Yayin da mu ke jiran su, sai wani sojan Isra’ila ya yi wa gungun mutane tsawa a gabanmu da suke ƙoƙarin komawa cikin kwantena domin duba ’yan’uwansu da aka tsare.
Ya yi amfani da lasifika ya ce su ci gaba da tafiya kuma su ba da tazarar akalla mita 300, sai wani soja ya fara harbin iska a kusa da su don razanasu su. Mun ji ƙarar harbe-harbe da yawa yayin da muke cikin layin.
Kowa yana kuka, mahaifiyata ta fashe da kuka: "Me ya faru da 'ya'yana? Sun harbe su ne?"
Bayan fiye da sa'a ɗaya 'yan'uwana sun bayyana.
Rundunar sojojin Isra'ila (IDF) ta shaida wa BBC cewa "mutane da ake zargi da alaƙa da ƙungiyoyin 'yan ta'adda ana tsare da su ne domin gudanar da bincike, kuma idan har aka ci gaba da tuhumar su a kan kai su Isra'ila don ci gaba da yi musu tambayoyi. Wasu kuma “an sake su cikin gaggawa”, in ji ta.
Ta ce dole ne a cire tufafi don bincikar bama-bamai ko wasu makamai kuma ana tufatar da fursunonin da wuri. Ta ce ba ta da nufin "gurɓata tsaro da kuma mutuncin waɗanda ake tsare da su" kuma IDF "tana aiki bisa ga dokokin ƙasa da ƙasa".
Har ila yau, IDF ta ce "ba ta harbin fararen hula da ke hijira daga arewa zuwa kudu", amma a lokacin da matasa suka yi kokarin matsawa akasin haka, "a kan yi yi harbi da nufin tarwatsa su, bayan da aka gargaɗe su da lasifika cewa kada su ci gaba tnkarar inda sojoji suke amma suka ci gaba da yin hakan”.
Ta ƙara da cewa ƙarar harbe-harbe ya zama ruwan dare kuma "ƙarar harbe-kaɗai ba ta nuni da cewa ana harbi daga wani wuri ne ko kuma wani irin nau'i".
Ni da matata mun sami kwanciyar hankali yayin da muka ci gaba da tafiya muka ƙara nisa daga shingen binciken, amma ba mu da masaniyar cewa akwai sauran wahala a gaba.

Yayin da muke tafiya kudu, na ga gawarwaki kusan 10 a wurare daban-daban a bakin hanya.
Ƙuda da tsuntsaye sun mamaye wasu ɓangarorin jiki da suka warwatse, kuma sun fara ruɓewa . Suna wani irin warin da ban taɓa jin irinsa ba.
Ban so yarana su ga waɗannan gawawwkin ba, sai na yi kururuwa, na ce su kalli sama su ci gaba da tafiya.
Na ga wata mota da ta kone tare da kan mutum a ciki. Hannun gawar da bata da kai tana rike da sitiyarin.
Akwai kuma gawawwakin jakuna da dawaki, wasu sun zama kwarangwal, da tarin tarkace da abinci da suka lalace.
Sai wata tankar yaƙin Isra'ila ta ɓullo akan wata hanya ta gefe, ta nufe mmu a guje. Muka firgita, yayin gudu, sai da muka tattaka gawawwaki. Wasu mutanen da ke cikinmu sun yi tuntuɓe da gawarwakin. Tankar ta sauya hanya kimanin Mita 20 kafin ta isa babban titin.
Nan da nan, aka jefa bam a wani gini da ke kusa da titin. Fashewar ta kasance mai ban tsoro kuma tarkace sun warwatsu a ko ina.
Na so duniya ta hadiye mu.
Mun girgiza ga kuma gajiya amma mun cigaba da tafiya zuwa sansanin Nuseirat. Mun isa can da yamma kuma dole ne mu kwanta a bakin hanya. Ana matuƙar sanyi.
Mun sanya rigar sanyi kan yaran mu biyu, muka cusa hannayensu cikin hannayen rigar don ƙoƙarin ɗumama su. Muka lullube ɗan autanmu da rigata. Ban taɓa jin sanyi irin wannan ba a tsawon rayuwata.
Da BBC ta yi tambaya game da tankar yaƙin da gawawwakin, rundunar ta IDF ta ce "a cikin yini, tankunan yaƙi na tafiya kan hanyoyin da suka haɗa da hanyar Salah al-Din, amma babu wani batu da tankunan da suka nemi afkawa fararen hula da ke tafiya daga arewa zuwa kudancin Zirin Gaza."
Rundunar IDF ta ce ba ta da labarin tarin gawawwaki a kan titin Salah al-Din amma akwai lokutan da motoci da suka fito daga Gaza suka yi watsi da gawawwaki yayin tafiya, wanda daga baya sojojin suka kwashe.
Neman hanyar tsira
Da gari ya waye mun tashi da wuri muka kama hanyan Khan Younis, birni na biyu mafi girma a Gaza. Mun biya wani ya ɗan rage mana hanya a cikin amalanke. Daga nan a Deir al-Balah, mun hau wata motar bas wadda aka yi niyyar daukar mutane 20 kawai, amma mutane 30 suka hau. Wasu suna zaune har a samar motar, wasu kuma suna maƙale a jikin ƙofa da tagogi daga waje.
A Khan Younis, mun yi ƙoƙari mu sami wurin da za mu zauna a makarantar da Majalisar Dinkin Duniya ta mayar da ita mafaka, amma ya cika. Mun ƙare da hayar wani ɗakin ajiye kayayyaki a ƙarƙashin wani gida inda muka zauna har tsawon mako guda.

Asalin hoton, Jehad El-Mashhrawi
Iyayena da ’yan’uwana maza da mata sun yanke shawarar zama a Khan Younis, amma bayan da aka jefa bam a kasuwar yankin, ni da matata muka yanke shawarar kai yaranmu kudu zuwa Rafah don su kasance tare da danginta. Sun yi s'ar samun motar da ta rage masu hanya ni kuma daga daga baya na nemi bas don in tarar da su, amma dai na samu ya cika sai na maƙale a jiƙin ƙofar.
Yanzu muna hayar wani ɗan ƙaramin gida wanda aka yi rufinsa da robobi. Babu wani abu da zai kare mu daga tarkacen da ke fadowa.
Komai ya yi tsada kuma ba za mu iya samun yawancin abubuwan da muke buƙata ba. Idan ana son ruwan sha, sai mu yi layi na sa'o'i uku, kuma ba mu da isasshen abinci da za mu ci sau uku a rana, don haka ba ma cin abincin rana, sai dai karin kumallo da abincin dare.
Na kan bai wa ɗa na kwai kowace rana. Kwai - wai ku ji fa? ko wannan ba zan iya ba shi ba yanzu. Abin da nake so in yi shi ne in bar Gaza in zauna lafiya da ’ya’yana, ko da hakan yana nufin zan zauna a cikin tanti.







