'Yan sanda sun rage wa amare hanya a mota

Asalin hoton, HAMPSHIRE CONSTABULARY
Wasu amare biyu da 'yan sanda suka rage wa hanya zuwa wurin bikinsu a lokacin da motar bas ɗin su ta samu matsala, sun ce jami’an da suka kuɓutar da su, sun yi matukar kokari.
Jemma da Sian Batchelor-Thomas sun kasance tare da 20 daga cikin danginsu da sauran makusantansu a lokacin da motar bas ɗinsu ta lalace a Hedge End da safiyar Asabar.
Jami’an sun rage wa amaren hanya zuwa bikin a cikin motar ‘yan sanda yayin da wasu suka hau wadansu motocin da ke wucewa.
Sun ce, duk da tsananin damuwa da aka shiga lokacin da lamarin ya faru, kowa ya isa wurin bikin kan lokaci.

Asalin hoton, HAMPSHIRE CONSTABULARY
Jemma ta ce: “Biki ne da babu mutane da yawa don haka muka yi hayar bas daga wurin da muka sauka don kowa ya sami walwala kuma ya ji dadin tafiyar.
“Amma dai hakan bai faru ba domin bayan mintuna 10 sai aka sami matsala.
“Baki sun dauka wasa mu ke yi.

Asalin hoton, JEMMA AND SIAN BATCHELOR-THOMAS
Sian ta ce, duk da halin da suka shiga, hankalin baki bai tashi ba.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ta ce: “Wata daga cikin tawagar mu ta ga motar ‘yan sandan ta tambaye su ko za su iya rage mana hanya.
Wasu baki biyu, wadanda suka gabatar da kansu a matsayin Mark da Tash, su ma sun tsaya don rage wa wasu daga cikin ayarin amaren hanya.
Jemma ta ce: "Sian ta nuna natsuwa sosai amma ni dai shiga matukar damuwa - na yi tunanin 'wannan mummunan abu ne' amma yanzu, idan muka waiwaya baya, za mu iya dariya kan lamarin.
"Mutane sun yi kokari wurin tausaya mana tare da yunkurin taimaka mana - kowa da kowa, da mutanen da suka ragewa 'yan bikin mu hanya. Mun samu saƙonnin taya mu murna da farin ciki daga mutrane da dama.
"Kasancewar mu ma'aurata jinsi ɗaya, abin ya ba da mamaki - saboda babu wanda ya furta munanan kalamai, kowa ya nuna mana matuƙar goyon baya.
"Haka kuma ya nuna cewa 'yan sanda suna yi wa kowa aiki kuma tare da kare al'umma. Rachel da Lucy [jami'an] sun yi matukar kokari wajen gudanar dai ayyukansu."
A cikin wani sako da suka wallafa a shafinsu na Facebook, PCSO Rachel Barry da PC Lucy Stoneley na rundunar 'yan sanda a unguwar Hedge End, sun ce: "Muna yi musu fatan alheri don samun kyakkyawar rayuwa mai cike da farin ciki, kuma muna matukar farin ciki cewa mun kasance a wurin don taimakawa."

Asalin hoton, JEMMA AND SIAN BATCHELOR-THOMAS











