Erik Ten Hag ya ci wasa na 50 a Man United

An wallafa

Erik ten Hag ya ci wasa na 50 a Manchester United da fara aiki, bayan da ya doke Fulham ranar Asabar.

United ta je gidan Fulham ta yi nasara cin 1-0 a wasan mako na 11 a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Bruno Fernandez ne ya ci kwallon, kuma daf da za a tashi daga karawar, hakan ya bai wa United maki ukun da take bukata.

Manchester United tana mataki na takwas da maki 18 a kan teburin Premier League, bayan da ta buga wasa 11.

Ten Hag, wanda ya fara aiki da kungiyar Old Trafford ranar 1 ga watan Yunin 2022, ya ja karawar wasa na 79 ranar Asabar.

Kawo yanzu tsohon kociyan Ajax, ya ci wasa na 50 da canajaras tara aka doke shi fafatawa 20.

Wannan shi ne karon farko da aka samu kocin da ya ci wasa da yawa a karancin fara aiki a kungiyar tun bayan shekara 118.

Mai rike da wannan bajintar a United shi ne Ernest Mangnail, wanda ya fara daukar babban kofi a kungiyar a 1908 a gasar rukunin farko.

Ya ci wasa 50 shima a jan ragamar karawa 79 a fafatawar da United ta doke Blackpool 1- 0 a Bloomfield Road a 1905.

Ten Hag ya ja wasa 49 a Premier League da cin karawa 26 da canajaras shida, yayi rashin nasara14 tun bayan da ya fara aiki a Old Trafford.

Haka kuma a karkashinsa United ta ci kwallo 70, yayin da aka dura mata 59 a raga.