Waiwaye: Garambawul ɗin ministoci da ɗaukewar wutar lantarki a arewacin Najeriya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi.

Tinubu ya sallami ministoci biyar tare da naɗa sabbi

.

Asalin hoton, Tinubu/Facebook

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sallami ministoci biyar tare da naɗa wasu sababbi bakwai da kuma sauya wa goma ma'aikatu.

Wata sanarwa da fadar gwamnatin kasar ta fitar a shafinta na X, ta nuna cewa ministocin da aka cire su ne;

Waɗanda aka sallama:

1-Barr. Uju-Ken Ohanenye; ma'aikatar harkokin mata

2- Lola Ade-John; ministan harkokin yawon buɗe idanu

3- Farfesa Tahir Mamman; ministan ilimi

4- Abdullahi Muhammad Gwarzo; ƙaramin ministan gidaje da raya birane

5- Dr. Jamila Bio Ibrahim; ministar matasa

Kiran sojoji su yi juyin mulki a Najeriya cin amanar ƙasa ne - Hedikwatar Tsaro

.

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Hedikwatar tsaron Najeriya ta gargaɗi ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi da ke kira ga sojoji su yi juyin mulki a ƙasar, tare da jaddada cewa yin hakan cin amanar ƙasa ne a ƙarƙashin kundin tsarin mulki.

Hukumomin sojin sun kuma ƙara jaddada biyayyarsu ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da ƙudurinsu na kare tsarin dumukuraɗiyya a ƙasar.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da darektan yaɗa labarai na hedikwatar tsaron, Birigediya Janar Tukur Gusau ya fitar, inda ya ce sojojin za su ci gaba da mayar da hankali a kan babban aikin da ya wajaba a kansu, wanda ya haɗa da kare yankin ƙasar tare da tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Darektan ya ƙara da cewa ya kamata masu neman sojoji su yi juyin mulki, kamar yadda aka gani a wani hoton bidiyo da ake ta yaɗawa, su sani cewa wannan abu cin amanar ƙasa ne a bisa tanadin kundin tsarin mulki.

Janar Gusau, ya kuma ce zaman lafiyar da aka samu a ƙasar a yanzu, ya samu ne sakamakon goyon bayan da shugaban ƙasar ke ba wa sojoji da kuma jajircewar shugabancin sojojin.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa sojojin tare da haɗin gwiwar sauran jami'an tsaro za su ɗauki dukkanin matakan da suka dace wajen hana duk wani yunƙuri na sauyin da ta hanyar kundin tsarin mulki ba.

Hedikwatar tsaron ta Najeriya ta fitar da wannan sanarwa ne, bayan da aka riƙa yaɗa wani hoton bidiyo a kwakin nan inda wasu ke kira ga sojoji su yi juyin mulki a Najeriyar.

Tangarɗa a layin lantarkin Ugwaji-Apir ce ta jawo rashin wuta a arewacin Najeriya - TCN

.

Asalin hoton, TCN

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya TCN ya ce tangarɗa aka samu a layin lantarki na Ugwaji-Apir mai ƙarfin 330kV, wanda ya yi sanadiyar rashin wuta a arewacin ƙasar.

Kamfanin ya ce matsalar ta shafi yankunan arewa maso gabas, da arewa maso yamma, da wasu ɓangarori na arewa ta tsakiya.

Wata sanarwa da kamfanin na Transmission Company of Nigeria ya fitar ta ce: "Da misalin ƙarfe 4:53 na safiya ne layin lantarkin Ugwuaji-Makurɗi na biyu mai ƙarfin lantarki 330kV ya samu tangarɗa, sai aka tura lantarki mai ƙarfin megawat 243 zuwa layi na ɗaya a layin domin ci gaba da samar da wutar.

"Sai shi ma da misalin ƙarfe 4:48 na safiyar ya samu matsala, wadda ta sa aka rasa lantarki mai yawan megawat 468. Da misalin ƙarfe 5:17, mun sake gwada layi na ɗaya da na biyun, amma dukkansu suka sake samun tangarɗa a tare."

A makon da ya gabata ne babban layin lantarki na Najeriya ya lalace har sau uku cikin kwana biyu, abin da ya jefa duka ƙasar cikin duhu.

Gwamnati ta ba Julius Berger mako ɗaya domin amincewa da kwangilar ƙarasa titin Kaduna-Abuja

.

Asalin hoton, Gwamnatin Najeriya

Ministan aikace-aikacen Najeriya, David Umahi ya ba kamfanin Julius Berger wa'adin mako ɗaya ya amince da naira biliyan 740.79 domin ƙarasa kilomita 82 na ɓangare na biyu na titin Abuja-Kaduna-Zaria-Kano.

Umahi ya bayyana hakan ne a lokacin da sabon manajan darakta na Julius Berger Plc, Dr Pier Lubasch ya kai ziyara ma'aikatar ayyuka tare da rakiyar tsohon manajan daraktan, Dr Lars Richter a Abuja.

A wata sanarwa da mai ba ministan shawara a kan harkokin watsa labarai, Orji Uchenna ya fitar a ranar Laraba, ya ce idan kamfanin bai amince da kwantiragin ba, za a iya ƙwace aikin.

"Ministan ayyuka Sanata Nweze David Umahi, ya buƙaci kamfanin Julius Berger ya amince da sabuwar yarjejeniyar aikin ƙarasa aikin na ɓangare na biyu na titin Abuja-Kaduna-Zaria-Kano a kan kuɗi naira biliyan 740, 797,204,713.25," in ji shi, inda ya ƙara da cewa rashin ƙarasa aikin ya jefa matafiya cikin ƙunci.

"Don haka idan Berger ba za su yi aikin ba, sai mu nemi kamfanin da zai ƙarasa aikin. Kuɗin kwangilar ya tashi daga naira biliyan 710 zuwa biliyan 740 saboda jan ƙafa da kamfanin ke yi, kuma idan aka ci gaba a haka, kuɗin zai ƙaru ne, wanda zai zama matsala ga ma'aikatar," kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

Gwamnonin Zamfara da Katsina sun gana da Ribadu da Badaru kan matsalar tsaro

.

Asalin hoton, Sulaiman Bala Idris

Gwamnonin jihohin Zamfara da Katsina Dauda Lawal da Dikko Radda sun yi wata ganawar sirri da ministan tsaro, Badaru Abubakar da kuma mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu a Abuja.

Ganawar da aka yi ranar Talata, bayanai na nuna cewa ta mayar da hankali ne kan samar da hanyoyin da za su haɗa ƙarfi da ƙarfe tar da duba sabbin hanyoyin da za a bi domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankunansu.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Zamfara Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya ce gwamnonin sun tattauna da ministan da mai ba shugaban ƙasar shawara ne a kan wasu shawarwari da haɗakar ƙungiyoyin arewa wato CNG suka gabatar domin samar da zaman lafiya a jihohinsu, da sauran abubuwan da suka shafi tsaro.

Taron ya kuma samu halartar shugaban kwamitin amintattu na NCG, Alhaji Nastura Ashir Shariff da sauran mambobin kwamitin tsaro na ƙungiyar.

Masu sayen abinci su ɓoye ne ke haifar da hauhawar farashi - Gwamnatin Najeriya

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata kasuwar sayar da kayan abinci a arewacin Najeriya

Hukumar kula da hakkin masu sayayya ta Najeriya, FCCPC ta zargi masu sayen kayan abinci su ɓoye da haifar da ƙaruwar hauhawar farashin kayan abinci a ƙasar.

Shugaban hukumar, Tunji Bello ne ya bayyana haka ranar Laraba a wani taron masu ruwa da tsaki a birnin Kano da ke arewacin ƙasar, kamar yadda jaridun ƙasar suka ruwaito.

Ya ƙara da cewa binciken da hukumarsa ta yi, ta gano yadda wasu 'yan kasuwa ke rububin sayen sabon kayan abinci da aka fara girbewa suna ɓoyewa, lamarin da ya ce yana ƙara ta'azzara ƙarancin abincin a kasuwanni, abin da kuma ya ce shi ke haifar da ƙaruwar hauhawar farashin kayyaki.

“Waɗannan mutane ba su damu da halin da al'ummar ƙasarmu za su shiga ba, don haka suke bi gonakin manoma suna sayen kayan a bincin da suka noma, ko su je kasuwanni suna sayen kayan abincin da aka tara domin su riƙa ɓoyewa, suna kuma safararsu zuwa ƙasashen waje don sayarwa a farashi mai tsada, wanda kuma hakan na jefa ƙasarmu cikin matsalar ƙarancin abinci,'' kamar yadda shugaban hukumar ya bayyana.

Babu wa'adin amfani da tsoffin takardun kuɗi - CBN

.

Asalin hoton, Getty Images

Babban Bankin Najeriya, CBN ya yi watsi da raɗe-raɗin da wasu ke yaɗawa a ƙasar cewa daga ranar 31 ga watan Disamba mai zuwa za a daina amfani da tsoffin takardun kuɗin ƙasar.

Cikin wata sanarwa da CBN ɗin ya fitar ranar Alhamis ya ce wannan iƙirari ba gaskiya ba ne kuma ba shi da tushe balle makama.

''Bisa hukuncin ci gaba da amfanin da tsoffin takardun kuɗin da kotun ƙolin Najeriya ta yi a ranar 29 ga watan Nuwamban 2023, ta ce a ci gaba da amfani da takardun ba tare da iyakancewa ba'', in ji sanarwar.

Haka kuma sanarwar ta yi kira ga bankunan ƙasar su ci gaba da mu'amala da tsoffin takardun kuɗin.