Madrid ta taya Olise Fam miliyan 188, Tottenham na harin Leao

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid na shirye shiryen taya ɗan wasan Bayern Munich, Michael Olise, da ake sa ran farashinsa zai kai euro miliyan 220 kwatankwacin fam miliyan 188. (Fichajes - in Spanish)
Tottenham na duba yiwuwar ɗauko ɗan wasan Ac Milan da Portugal Rafael Leao, da ke shirye ya kaoma Landon. (Teamtalk)
Babu tabbasa a makomar Bradley Barcola a Paris St-Germain, yayin da Arsenal da Liverpool ke zawacin ɗan wasan. (Talksport)
Newcastle na harin ɗan wasan Jamus da Stuttgart Angelo Stiller, a mastyin ɗan wasan da zai ƙara ƙarfafa tsakaiyar ƙungiyar. (Bild - in German)
Manchester United na sanya ido kan mai tsaron ragar Paraguay da San Lorenzo, Orlando Gill. (Fichajes - in Spanish)
Ɗan wasan Liverpool da Netherlands Cody Gakpo, da ɗan wasan Manchester City da Brazil Savinho, na daga cikin ƴan wasan da Tottenham ke son ɗauka a kakar wasanni. (Talksport)
Juventus, da Fiorentina, da Brentford, da Brighton, da RB Leipzig na zarwarcin ɗan wasan Trabzonspor da Ivory Coast Christ Inao Oulai. (La Gazzetta dello Sport - in Italian)
Ɗan wasan Tottenham Radu Dragusin zai koma Fiorentina, a matsayin ɗan wasan aro, da shirin siyen ɗan wasan na ƙasar Romaniya, kan fam miliyan 21.4 idan har suka cika ƙa'ida. (Sky Sports)
Hull City na son siyen mai tsaron ragar Napoli da Serbia Vanja Milinkovic-Savic, yayin da suka fara shirye-shiryen komawa buga gasar Firimiya. (Corriere dello Sport - in Italian)
Ɗan wasan Sporting da Portugal Gonçalo Inaci, na cikin jerin ƴanwasan da AC Milan ke son ɗauka, don ƙara inganta tsaron bayanta, a kakar wasa mai zuwa. (Fichajes - in Spanish)
Ɗan wasan Chelsea da Ingila Trevoh Chalobah, ya fi son komawa Inter Milan a wannan kaka. (La Gazzetta dello Sport - in Italian)














