Man United za ta kara rage ma'aikata tsakanin 100 zuwa 200

Asalin hoton, Getty Images
Ɗaya daga wanda ya yi hadakar mallakar Manchester United, Sir Jim Ratcliffe na duba yiwuyar yadda za a kara rage ma'aikatan ƙungiyar.
Wata majiya ta tabbar da cewar United na duba yadda za ta kara rage kuɗin da take kashewa da zai kai £300m a shekara uku.
United ba ta ce komai ba kan rahoton cewar Ineos Group, karkashin Ratcliffe na auna yadda zai sake rage ma'aikata kimanin 100 zuwa 200 ba.
Daga baya ne za a fayyace yawan ma'aikatan da za a rage da guraben da suke aiki, domin aiwatar da shirin.
Haka kuma United za ta rufe ofishinta da ke Landan a Kensington, amma ta sanar cewar za ta ci gaba da kasancewa a cikin birnin don hulɗar kasuwa.
Tun farko United ta rage ma'aikata 250 da cire butum butumin Sir Alex Ferguson a matakin jakadan da ake biya da soke biyan kuɗi ga ma'aikata, domin zuwa kallon wasan karshe.
United ta ce za ta yi amfani da kuɗin da za ta samu daga rage ma'aikatan, wajen bunkasa babbar ƙungiyar da sauran ayyuka.
Ƙungiyar ta Old Trafford ta ce kuɗin da za ta samu zai kai £45m a kowacce shekara daga ragge ma'aikatan.
Haka kuma wani babban jami'in ƙungiyar da ya dade kan mukamin kula da gudanar da United, Jackie Kay wanda yake Old Trafford shekara 30 zai ajiye aikin.
Wasu rahotannin na cewar Ratcliffe ya zuba kudin da ya kai £300m a United, domin bunkasa filin atisaye na Carringhton da tsara yadda za a fuskanci gina sabon sitadiya.
Ana jiran Ratcliffe ya bayar da izinin fara shirin gina sabon filin da za a kashe £2bn, ko kuma a yi wa Old Trafford kwaskwarima da zai ci £1.5bn
United ta sanar da yin hasarar kasuwanci da ya kai £113.2m daga ranar 30 ga watan Yunin 2024.
United tana ta 13 a teburin Premier League, bayan wasan mako na 24.










