Gomez ya koma yin atisaye tare da ƴan wasan Liverpool

Asalin hoton, Getty Images
Mai tsaron bayan Liverpool, Joe Gomez ya koma atisaye tare da ƴan wasan ƙungiyar bayan jinya, hakan karin karfin gwiwa ne ga koci, Arne Slot.
Gomez, mai shekara 27, bai yi wa Liverpool karawa bakawi ba, tun bayan da ya ji rauni a wasan West Ham ranar 29 ga watan Disambar 2024.
Mai tsaron bayan ya murmure lokacin da Liverpool ke shirin fuskantar PSV Eindhoven a wasan karshe a cikin rukuni a gasar zakarun Turai ranar Laraba a Netherlands.
Sai dai Curtis Jones, wanda bai buga wa Liverpool wasan Premier da ta doke Ipswich ba a karshen mako da Diogo Jota har yanzu suna jinya.
Rashin Gomez ya sa Slot na amfani da matashi mai shekara 21, Jarell Quansah ko kuma Ibrahima Konate da yake haɗa su da ƙyaftin, Virgil van Dijk.
Watakila Gomez ya bi Liverpool wasan PSV, amma dai kila ya yi zaman benci, domin ya samu ya murmure sosai.
Liverpool wadda ta ci wasa bakwai a Champions League a fafatawar rukuni na bukatar maki ɗaya domin ta ci gaba da zama ta daya a kan teburi.
To sai dai Liverpool ta kwan da sanin za ta je Bournemouth a Premier League ranar Asabar, karawa ce da za ta yi tsauri.
Kenan watakila ta ajiye wasu manyan ƴan wasa a Champions League, domin ta fuskanci Bournemouth ranar Asabar 1 ga watan Fabrairu.











