Real Madrid ta bai wa Granada aron Reinier

Asalin hoton, EPA
Real Madrid ta cim ma yarjejeniyar bai wa Granada aron ɗan wasan tsakiyarta Reinier Jesus tsawon kaka ɗaya.
Rahotonni sun ce ƙungiyoyi daga gasar Championship ta Ingila sun nemi ɗaukar ɗan wasan mai shekara 22, cikinsu har da Norwich amma kuma yanzu zai cigaba da zama a La Liga.
Reinier ya koma Real a 2020 daga Flamengo ta Brazil kan fan miliyan 25 amma kuma bai taɓa buga wa babbar ƙungiyar wasa ko ɗaya ba.
Ya shafe shekara huɗu da rabi yana buga wasannin aro a Borussia Dortmund, da Girona, da kuma Frosinone.
Da aka tambaye shi game da Reinier kafin wasansu da Las Palmas ranar Alhamis, kociya Carlo Ancelotti ya ce: "Shawarar da zan bayar ita ce [ya koma] wata ƙungiyar da zai iya nuna kansa."
Duk da ƙarancin buga wasa da kuma rauni, Reinier ya ci ƙwallo biyar kuma ya bayar da huɗu an zira a raga a ƙungiyoyin uku da ya je wasa aro.
Sai dai har zuwa yanzu da ya tafi Granada, ba shi da lamba a Real kuma ƙaramar tawagar ƙungiyar kawai ya taɓa buga wa wasa.








