Ƙwazon Salah zai yi tsada lokacin tsawaita yarjejeniya a Liverpool

Slot Salah

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Koci, Arne Slot ya ce ƙwazon da Mohamed Salah ke yi a wasannin bana, zai kara yin tsada idan Liverpool za ta tsawaita ƙwantiraginsa.

Ɗan wasan tawagar Masar zai cika shekara 33 da haihuwa cikin watan Yuni lokacin da yarjejeniyarsa za ta kare da ƙungiyar ta Anfield.

To sai dai ɗan ƙwallon, yana taka rawar gani a kakar nan fiye da bajintar da ya yi a ƙungiyar a kakar 2017.

Shi ne ya karɓi ƙyautar fitatcen ɗan wasa a karawar da Liverpool ta doke Manchester City 2-0 ranar Lahadi a Etihad a Premier League.

Hakan ne ya sa Liverpool ta ci gaba da zama ta biyu a kan teburin Premier da tazarar maki 11 tsakani da Arsenal ta biyu da tazarar maki 20 tsakani da City ta huɗu.

A wasan ne Salah ya ci ƙwallo, sannan ya bara da na biyu aka zura a raga, ya zama na farko da ya yi wannan bajintar gida da waje a kan wadda ke rike da kofin Premier League a kaka ɗaya.

Salah ya ci ƙwallo 30 a kakar nan 25 daga ciki a Premier League, na farko da yake da hannu a cin ƙwallo 40 ko fiye da haka a kaka biyu a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Haka kuma shi ne kan gaba mai hannu a cin ƙwallo 50 a dukkan karawa a bana tsakanin manyan gasar Turai biyar.

Liverpool tana da wani tsari da take taka tsantsan kan tsawaita yarjejeniya da duk wani ɗan wasanta da ya kai shekara 30 da haihuwa.

Liverpool, wadda take jan ragamar teburin Premier League za ta karɓi bakunci Newcastle ranar Laraba.

Daga nan za ta je Paris St Germain wasan zagaye na biyu a Champions League ranar Laraba 5 ga watan Maris.