Matsayar cocin Katolika kan zaɓen Kamaru, bayan Bakary ya yi iƙirarin nasara

    • Marubuci, Paul Njie
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa, Yaoundé
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 3

Cocin Katolika mai ƙarfin faɗa a ji a Kamaru ta yi kiran a kwantar da hankali yayin da ake hasashen ɓarkewar rikici bayan sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar.

Ɗan takarar adawa kuma tsohon kakakin gwamnati, Issa Tchiroma Bakary ya ayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen ranar 12 ga watan Oktoba, yana mai cewa ya doke shugaba Paul Biya mai shekara 93 wanda ke neman ƙarin wa'adin mulki na shekara bakwai bayan shafe shekara 43 kan mulki.

Sanarwar Tchiroma ta fuskanci suka daga gwamnati da kuma jam'iyyar shugaba Biya yayin da wasu ke ganin ya saɓa ƙa'ida.

Majalisar kundin mulkin Kamaru ba ta kai ga sanar da sakamakon zaɓen ba.

Majalisar na da zuwa ranar 27 ga watan Oktoba kafin sanar da wanda ya yi nasara a zaɓen.

Jajircewar da Tchiroma mai shekara 76 ya yi da kuma shan alwashin kare nasarar da yake iƙirarin yi a zaɓen ya janyo zaman ɗar-ɗar a ƙasar da ke tsakiyar Afirika.

A wata sanarwa, kwamitin limaman ɗarikar Katolika na National Episcopal Conference of Cameroon (NECC), ya bayyana buƙatar zaman lafiya da daidaito a ƙasar.

Limaman Katolikan sun ce suna fata sakamakon zaɓen zai fitar da haƙiƙanin gaskiyar da masu zaɓe ke fata, kuma sun yi fatan "hukumomi ba za su canza sakamakon zaɓen ba".

Ana matuƙar mutumta cocin Ktolika a Kmaru kuma mata kallon wata mai ƙarfin faɗa a ji a ƙasar.

Sanarwar cocin ta ƙara jaddada kiran da wasu da dama a ƙasar ke yi inda suke neman a tabbata ba a tafka magudi ba wajen bayyana sakamakon zaɓen.

Wasu limaman cocin sun yi suna wajen sukar Shugaba Biya da kuma salon mulkinsa.

A watan Janairu Bishop Monsignor Yaouda Hourgo, daga yankin Arewa mai nisa ya ce gara ''sheɗan'' ya ƙwace mulki a kan sake zaɓen shugaba Biya.

"Mun riga mun wahala, mun gaji,'' in ji Bishop ɗin.

Bayan zanga-zangar da aka yi domin bayyana damuwa kan tafka maguɗi, majalisar kundin mulkin ƙasar ta ce za ta fara sauraron ƙorafi game da zaɓen a ranar Laraba. Matsayar ta na da tasiri kan sakamakon zaɓenKamaru.

A saƙon su ga alƙalan majalisar, limaman cocin Katolikan sun jaddada matsayar su cewa dole a bari ''Gaskiya ta yi halin ta.''