Ban taɓa samun farin ciki a PSG ba - Messi

Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Lionel Messi ya ce ya yanke shawarar komawa taka leda a Inter Miami, saboda baya samun farin ciki lokacin da ya taka leda a Paris St-Germain.

Mai shekara 37, ya lashe Ligue 1 karo biyu da Fench Cup a 2022 a kaka biyu da ya yi a PSG, daga baya ya bar ƙungiyar a 2023.

''Sa hannu da na yi da Inter Miami dama ce, saboda wasu abubuwan da suka faru a bara a Paris,'' in ji mai ballon d'Or takwas a hirar da ya yi da Apple Music ranar Juma'a.

''Hukunci ne da ya kamata na ɗauka, saboda na bar Barcelona, sannan na yi kaka biyu ba tare da ina jin daɗi ba.'' kamar yadda ƙyaftin ɗin Argentina ya sanar.

''Ba na farin ciki kwana biyu a jere tun daga wajen atisaye da buga gasa, na kasa sabawa da abubuwa da yawa.''

Messi, wanda ya lashe La Liga 10 da Champions League huɗu da Club World Cup uku a Barcelona ya bar ƙungiyar a 2021.

Hakan ya biyo bayan da Barcelona ba za ta iya biyan ɗawainiyar Messi ba, wanda ya kara rattaba ƙwantiragin ci gaba da taka leda kaka biyu a ƙungiyar.

Dalilin da ya sa ya zama wajibi Messi ya koma Paris St Geramin kan yarjejeniyar kaka biyu.

Bayan da Messi ya ja ragamar Argentina ta lashe kofin duniya a Qatar a 2022, sai magoya bayan PSG suka juwa masa baya, sakamakon rashin kokarin ƙungiyar a Champions League.

Haka kuma an dakatar da shi, saboda zuwa Saudi Arabia ba tare da izinin mahukuntan PSG ba da ta kai bai samu halartar atisaye ba.

Ɗan wasan tawagar Argentina, wanda ya koma Inter Miami, bayan tayi mai tsoka daga manyan ƙungiyoyi ya ce ''Na koma Amurka ne domin na taimakawa gasar kasar ta kara bunkasa a duniya.''