Alamomi biyar da za ku gane ƙodarku na da matsala

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Ƙoda na aiwatar da muhimman ayyuka da dama a jikinmu a lokaci guda, kuma suna fitar da tarkace daga jikin, tare da daidaita ruwan jiki.

Haka kuma suna sa ido kan hawa da saukar jini sannan suna taimakawa wajen samar da jajayen ƙwayoyin jini.

Duk da waɗannan muhimman ayyukan da ƙoda ke yi a jiki, mutane da dama sukan yi watsi da alamomin farko na gazawar ƙoda ko cutar ƙoda.

Idan aka gano waɗannan alamomi da wuri, ana iya fara magani na cututtukan da suka shafi koda tun da wuri.

Ga wasu alamomi guda biyar da ake yawan yin sakaci da su, alhali kuwa suna iya zama alamar cutar ƙoda ko gazawarta.

Yawan fitsari

Idan ƙoda ta lalace, jikin mutum ba ya fitar da fitsari yadda ya kamata, sai a ga mutum yana yawan jin fitsari.

Sau da yawa ana gane hakan ta hanyar bayyanar kumfa a fitsari.

''Amma wannan ba wajibi ba ne, wasu cututtuka ma na iya haifar da kumfa a fitsari'', in ji Dr. Mohsin Wali, babban likita a Asibitin Sir Gangaram.

Kumburi a jiki

Likitan ya ce kumburin ido da ƙafa na iya zama alamar gazawar ƙoda.

''Idan ƙafafunka suka kumbura, bai kamata ka yi sakaci da hakan ba, domin yana nuna akwai alamun matsalar ƙoda'', in ji shi.

Karima Agarwal, ƙwararriyar likitar koda a Asibitin Manipal, ta ce: "Ya kamata mutum ya yi taka-tsantsan idan ƙafafunsa suka kumbura.

Kumburin ido da fuska da ƙafa na nuna cutar ƙoda."

Hawa da saukar jini

A cewar ƙwararru, "hawa da saukar jini mai tsanani na iya shafar ƙoda."

Haka kuma, gazawar ƙoda na iya haifar da ƙaruwar hawa da saukar jini.

Saboda haka, ya kamata a yi taka-tsantsan game da hawa da saukar jini.

"Sau da yawa, hawa da saukar jini baya samun kulawa yadda ya kamata, sai dai ai ta ƙara yawan magungunan da aka bai wa mutum.

''Wannan ma yana iya zama alamar cutar koda," in ji Dr. Garima Agarwal.

Ciwon suga

Ciwon suga na cikin abun da ke haddasa ciwon ƙoda.

Dr. Garima Agarwal ta bayyana cewa kashi 80 cikin 100 na masu ciwon ƙoda suna fama da ciwon suga.

Ciwon ƙoda yana shafar kashi 30 zuwa 40 cikin 100 na mutane masu ciwon suga.

Idan masu ciwon suga suka fara samun alamun ciwon ƙoda, matakin sukarin jini nasu kan ragu.

Ciwon ƙoda yana fara bayyana ne idan matakin sukari a jiki ya yi yawa na tsawon shekaru da dama.

5. Gajiya, jin ƙaiƙayi da jin amai

Gajiya da jin ƙaiƙayi a jiki, da amai na iya zama alamun ciwon ƙoda.

Masana sun bayyana cewa jin ƙaiƙayi yana faruwa ne sakamakon rashin sinadarin phosphorus a jiki saboda ciwon koda na haifar da ƙarancin phosphorus a jiki.

Wasu marasa lafiya masu ciwon ƙoda kan fara jin amai ko rashin sha'awar abinci.

Masana sun ce yin rayuwa mai kyau na iya taimakawa sosai wajen hana ciwon ƙoda.

Yadda za ku kare kanku daga ciwon ƙoda

Dr. Mohsin Wali da Dr. Karima Agarwal sun bayyana wa BBC hanyoyi guda shida na kare kai daga kamuwa da ciwon ƙoda, sun haɗa da.

Shan wadatacecn ruwa

Ruwa na taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye lafiyar ƙoda.

Idan mutum na shan isasshen ruwa, ƙodarsa na samar da fitsari mai yawa wanda ke taimakawa wajen fitar da abubuwan cutarwa daga jiki.

Haka kuma, hakan na rage haɗarin samuwar duwatsun ƙoda da kamuwa da cututtuka.

''Idan kana shan isasshen ruwa, fitsarinka zai kasance mai tsabta ko mai launin ruwan ɗorawa mai haske''.

Dr. Garima Agarwal ta ce ya kamata mutum ya sha lita biyu da rabi na ruwa a kowace rana.

Rage cin gishiri

Yawan gishiri ba shi da kyau ga ƙoda saboda yana ƙara hawa da saukar jini kuma yana lalata ƙodar.

A guji cin pickles da abinci da aka sarrafa.

Abinci kamar noodles yana da yawan gishiri, don haka a kauce masa.

Rage shan sukari

Idan kana son kauce wa ciwon ƙoda, ka rage shan kayan zaƙi, kamar yadda likitocin suka yi ƙarin haske.

Sukari na kara ƙiba kuma yana ƙara haɗarin kamuwa da ciwon ƙoda.

Kula da nauyin jikinka

Idan kana son kauce wa ciwon ƙoda, ka kula da nauyin jikinka ta hanyar motsa jiki.

Masana sun ce mutanen da suka yi ƙiba su rage nauyi saboda suna cikin haɗarin kamuwa da ciwon koda.

Cin abinci mai gina jiki

Ci abinci mai gina jiki da 'ya'yan itace yana kiyaye kamuwa da ciwon ƙoda.

Abincin da ke ɗauke da sinadarin probiotics na da kyau ga lafiya, don haka a basu fifiko.

A guji cin abincin da aka fiye soyawa.

''Shan isasshen ruwa, cin abinci mai gina jiki, da motsa jiki zai kiyaye lafiyar ƙodarka da kuma lafiyar jikinka gaba ɗaya'', in ji shi.

Kada ka sha magani ba tare da tambayar likita ba

"Mutane da dama suna saye da amfani da magunguna daga shagunan sayar da magani ba tare da tuntuɓar likita ba, in ji Dr. Karima Agarwal.

"Tsofaffi kan sha maganin ciwo saboda ciwon jiki da ciwon ƙashi''.

Wasu magungunan na iya ɗauke da sinadarai masu nauyi da steroids. Wannan na iya lalata kodar," in ji Karima Agarwal.