Cutuka biyar da ake ɗauka lokacin damina da yadda za a kauce musu

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Lokacin damina lokaci ne da ke kawo annashuwa da sauƙin zafi da yawancin mutane ke jira da fatansa.

Manoma kan yi marmarin lokacin domin shuka, yara don wasa a ckin ruwan sama, matasa don jin daɗin sanyi da iska.

A wannan lokacin yanayi kan sauya, ruwa kan cika rijiyoyi da madatsun ruwa, lamarin da ke sa a wasu lokuta a samu ambaliya ruwa, wani abu da ke kawo haɗari ga lafiyar ɗan'adam.

A duk lokacin da ruwan sama ya fara sauka, mutane da dama kan fuskanci matsalolin rashin lafiya daban-daban.

Amma waɗanne irin cututtuka ne suka fi yaɗuwa a wannan lokaci na damina, kuma yaya za a kare kai da iyali daga kamuwa da su?

Domin amsa wannan tambayar BBC ta tuntuɓi Dakta Nasir Ahmad, ƙwararren likita a ɓangaren kula da lafiyar jama'a a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja, domin fahimtar irin waɗannan cututtuka da yadda jama'a za su kare kansu da 'yan uwansu.

Waɗanne cutuka ne suka fi yaɗuwa?

Likitan ya lissafo cutuka da suka fi yaɗuwa a lokacin damina kamar haka

Zazzaɓin cizon sauro (maleriya): Dakta Ahmad ya ce zazzabin cizon sauro shi ne jagoran cututtukan damina.

A duk lokacin da ruwa ya fara taruwa cikin mazurari da shara, sauro na samun damar haihuwa cikin sauƙi.

Wannan yana barazana ga yara da mata masu juna biyu.

"A kowane sati, muna karɓar yara fiye da 100 da ke fama da malaria. Yawanci ba a kawo su asibiti sai cutar ta tsananta." in ji likitan.

Ciwon ciki da amai da gudawa (kwalera): Lokacin damina na yawan kawo gurɓataccen ruwa wanda ke haddasa cutuka masu aka da ciwon ciki, kamar amai da gudawa da zazzaɓin taifod.

Wannan na yawan shafar yara, musamman 'yan kasa da shekara biyar.

Dakta Ahmad ya ce "Yara na da rauni a garkuwar jikinsu, kuma idan suka kamu da gudawa, jiki na rasa ruwa cikin sauri, har ya kai ga mace-mace."

Ƙaiƙayi da ƙurajen fata: Likitan ya ce lokacin damina na kawo danshi, wanda ke haddasa ƙaiƙayi da tabo-tabo a fata da gashi da ƙurarraji wanda ke yaɗuwa cikin yara da matasa.

"Mafi yawan yara da manya da ke zuwa asibiti a lokacin damina suna fama da ƙaiƙayin fata da ƙurarraji a jiki." a cewar Dr. Ahmad.

Mura da tari da ciwon maƙogwaro: Sanyin damina da iska mai danshi na haddasa mura da tari, musamman ga yara da tsofaffi.

Yana iya haifar da matsanancin ciwon maƙogwaro da kamuwa da cututtukan numfashi kamar pneumonia.

"Yaro da manya da ba su da rigar sanyi ko suna yawan shan ruwan sanyi a damina, na iya fara tari da hanci mai yoyon majina." in ji likitan.

Ciwon Ido (Apollo - Conjunctivitis): Ciwon ido na "Apollo" yana yaɗuwa sosai a lokacin damina.

Idanun su kan yi ja, su kumbura, su riƙa zubar da ruwa, kuma suna yin zafi.

"Apollo yana yaɗuwa ne ta hanyar hannu da kuma amfani da kayayyaki irin su tawul ko gado tare da mai cutar." likitan ya ƙara da cewa.

Mene ne alamomin cutukan damina?

Dr. Ahmad ya lissafo alamomin waɗannan cututtuka kamar haka:

Alamomin zazzaɓin cizon sauro

  • Zazzabi mai tsanani
  • zafin jiki
  • Jin sanyi da zufa
  • Ciwon kai da kaikayin jiki
  • Yawan gajiya

Alamomin ciwon ciki da amai da gudawa (kwalera)

  • Yawan zuwa bayan gida
  • Ciwon ciki
  • Aman da ya ƙi tsayawa
  • Rashin ƙarfi da gajiya
  • Bushewar baki da fata

Alamomin ƙurajen fata da ƙaiƙayi

  • Ƙaiƙayi da kalar ja a fata
  • Ƙuraje na yin tsiro a kan fata har wasu suna ruwa da fashewa
  • Saurin fushi ko kukar yara saboda jin zafi

Alamomin mura da tari da ciwon maƙogwaro

  • Tari da mura
  • Zafi a maƙogwaro
  • Toshewar hanci
  • Yawan nishi da jin nauyi a ƙirji

Alamomin ciwon Ido (Apollo - Conjunctivitis)

  • Jan ido da kumburi
  • Zubar da ruwa ko kwantsa daga ido
  • Jin kaikayi a ido

Matakan kariya

Likitan ya bayar da shawarwari kan matakan kariyar da mutane za su ɗauka domin guje wa kamuwa da ɗaya daga cikin waɗannan cututtuka.

Matakan kariya daga zazzaɓin cizon sauro

  • Amfani da gidan sauro da aka shafa wa magani
  • Kawar da ruwa da shara a kusa da gida
  • Feshe wurin bacci da maganin sauro
  • Guje wa fita da dare ba tare da tufafin da ke rufe jiki ba

Matakan kariya daga ciwon ciki da amai da gudawa (kwalera)

  • Tafasa ko tace ruwan sha
  • Guje wa shan ruwa daga rafi ko rijiya mara rufi
  • Wanke hannu da sabulu kafin cin abinci da bayan-gida
  • Rage cin abinci daga titi ko inda ba a san yanayin tsaftarsu ba.

Matakan kariya daga ƙurajen fata da ƙaiƙayi

  • Wanka da ruwa mai tsafta sau biyu a rana
  • Busar da jiki sosai bayan wanka
  • Gujewa saka kaya masu nauyi ko waɗanda ke ɗame fata
  • Kar a riƙa amfani da tawul, soso ko man jiki tare da wani.

Matakan kariya daga mura da tari da ciwon maƙogwaro

  • Sanya rigar sanyi, musamman da dare
  • Shan ruwa mai ɗumi da shayi
  • Guje wa zama cikin iska
  • Kula da tsaftar hanci da bakin

Matakan kariya daga ciwon Ido (Apollo - Conjunctivitis)

  • Wanke hannu akai-akai
  • Gujewa taba ido da hannu mara tsafta
  • Kar a riƙa amfani da mayukan ido ko tawul na wani
  • A nisanci wanda ke ɗauke da ciwon ido har sai ya warke

Lokacin damina lokaci ne da ke ɗauke da albarka amma a lokacin guda kuma cike da haɗari ga lafiyar ɗanadam.

A cewar Dr. Ahmad, "Idan aka kula da tsafta, aka wayar da kan al'umma da iyaye musamman mata da ke kula da yara, za a rage kamuwa da waɗannan cututtuka da kaso mai yawa."