Zan kara nazartar ƴan wasa na a karawa da Southampton - Amorim

Asalin hoton, Getty Images
Ruben Amorim ya ce wasan da zai fuskanci Southampton ranar Alhamis a Premier, zai kara sa ya ci gaba da nazartar ƴan wasansa.
Hakan zai tantance ƙwazon ƴan ƙwallon United kan rawar da suka taka a gidan Liverpool da bajintar da suka yi a filin Arsenal a Emirates.
Bayan da United ta yi rashin nasara a wasa huɗu a jere, sai aka yi hasashen za ta ƙwaso ƙwallaye a Anfield, amma sai suka tashi 2-2.
Haka ma United ta kai zagaye na huɗu a FA Cup, bayan doke Arsenal a bugun fenariti a Emirates da cin 5-2, bayan da suka tashi 1-1, har da korar ɗan wasanta.
Saboda haka za a sa rai cewar United za ta yi abin kirki a karawa da Southampton, wadda take ta karshen teburi mai maki shida daga fafatawa 20 a kakar nan.
Amorim ya ce ''A wasan da muka yi da Liverpool da Arsenal, ƴan wasa sun jure da dukkan kalubalen da suka fuskanta, sannan suka kara sa ƙwazo da juriya.''
Kociyan ɗan kasar Portugal ya ce har yanzu yana ta gwaje-gwajen da zai kai ƙungiyar matakin da ya dace da ita.
Tun kan United ta je Anfield da Emirates ta yi rashin nasara a hannun Bournemouth da Newcastle da wanda Wolverhampton ta doke ta 2-0.
Amorim bai ce komai ba kan tambayar da aka yi masa kan makomar Marcus Rashford, bayan da ake alakanta mai shekara 27 da wasu manyan ƙungiyoyin.











