Liverpool ta amfana da zuwa PSG a Champions League

Elliot

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Liverpool ta je ta yi nasara a kan Paris St Germain da cin 1-0 a wasan farko zagayen ƴan 16 a Champions League ranar Laraba a Faransa.

Sauran minti uku a tashi daga karawar Liverpool ta ci ƙwallo ta hannun Harvey Elliott.

Wannan shi ne karo na biyar da suka kara a tsakaninsu a gasar zakarun Turai, inda Liverpool ta yi nasara ta uku, Paris St Germain ta ci wasa biyu.

Wasan da aka buga tsakanin PSG da Liverpool:

2024/2025

Champions League ranar Laraba 5 ga watan Maris 2025

  • Paris St-Germain 0 - 1 Liverpool

2018/2019

Champions League ranar Laraba 28 ga watan Nuwamba 2018

  • Paris St-Germain 2 - 1 Liverpool

Champions League ranar Talata 18 ga watan Satumbar 2018

  • Liverpool 3 - 2 Paris St-Germain

1996/1997

Euro Cup Winners Cup ranar Alhamis 24 ga watan Afirilun 1997

  • Liverpool 2 - 0 Paris St-Germain

Euro Cup Winners Cup ranar Alhamis 10 ga watan Afirilu 1997

  • Paris St-Germain 3 - 0 Liverpool

Ranar Talata 11 ga watan Maris, Liverpool za ta karɓi bakuncin wasa na biyu zagayen ƴan 16 a Champions League a Anfield.

Liverpool tana da Champions League shida da ta ɗauka 1977 da 1978 da 1981 da 1984 da 2005 da kuma 2019, ita kuwa PSG ba ta taɓa lashe kofin zakarun Turai ba.

Liverpool na fatan ɗaukar kofi uku a bana, wadda za ta buga wasan karshe a Carabao Cup da Newcastle United a watan nan.

Haka kuma ƙungiyar Anfield tana ta ɗaya a kan teburin Premier League da tazarar maki 13 tsakani da Arsenal ta biyu.