Casemiro na son komawa United in ji Ancelotti

Casemiro ya koma Real ne a 2013 ya ci La Liga uku da Champions biyar

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya ce dan wasan tsakiya na kungiyar Casemiro na son barin kungiyar zuwa Manchester united, wani ciniki da ake sa ran zai kai fan miliyan 59.2 kwatankwacin yuro miliyan 70.

Ana samun ci gaba a tattaunawa kuma United na da kyakkyawan fatan cewa cikin zai yiwu nan da yan kwanaki kalilan.

Dan wasan Brazil din mai shekara 30 ya yi atisaye da Madrid a ranar Juma’a.

“Ana ci gaba da tattaunawa a halin yanzu, har yanzu kuma dan wasanmu ne amma yana son tafiya,” in ji Ancelotti.

“Na tattauna da shi. Kan abin da ya yi a matsayinsa na Casemiro dole um girmama abin da yake so.”

Kocin dan kasar Italiya ya ce ‘‘Casemiro na son sauya sheka kuma mun fahimci hakan, ina zaton bai kamata um dakile shi ba.”

Asalin kudin da United za ta biya kan dan wasan bai fi yuro miliyan 60 ba, amma akwai karin miliyan 10 na sauran tsarabe-tsarabe.

Dan wasan ya koma Real Madrid ne a 2013, ya ci La Liga uku ya kuma lashe Champions biyar.

United da ke kasar teburin Premier z ata karbi bakuncin Liverpool a ranar Litinin.