Za a auna koshin lafiyar Zouma a Al-Orouba ta Saudi Arabia

Asalin hoton, Getty Images
Za a auna koshin lafiyar ɗan wasan West Ham, Kurt Zouma a shirin da yake na komawa Al-Orouba ta Saudi Arabia.
Tun farko Zouma ya kusan komawa Haɗadɗiyar Daulal Larabawa da taka leda a bana, sai aka samu matsala a lokacin da aka gwada koshin lafiyarsa.
West Ham ta bai wa mai tsaron bayanta izinin da ya ci gaba da zama a can har sai wakilansa sun samar masa wata ƙungiyar da zai koma da taka leda.
Har yanzu ba a kai ga cimma kwantiragi ba, an dai san za a auna koshin lafiyarsa, sannan West Ham ta amince ya koma wata ƙungiyar domin ya gwada sa'a.
Zouma, mai tsaron bayan tawagar Faransa ya buga wa West Ham wasa 103, tun bayan da ya koma ƙungiyar daga Chelsea kan £29m a 2021.
Ya buga wasan karshe a Europa Conference League a 2023 da ta lashe kofin, bayan doke Fiorentina.
Haka kuma an naɗa shi ƙyaftin din West Ham a kakar 2023/24, bayan da Declan Rice ya koma Arsenal.







