Watakil Salah zai koma Saudiyya, Arsenal na neman Gyokeres

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Saudiyya ta yi wa Dan wasan gaba na Masar, mai taka leda a Liverpool Mohamed Salah gagarunin tayin fam miliyan 65 idan ya koma can a lokacin bazara.(Sun)

Real Madrid ma na zawarcin dan wasan Liverpool kuma mai tsaron baya na Ingila, Trent Alexander-Arnold mai shekara 26, a lokacin bazara. (Relevo)

Arsenal na duba yiwuwar dauko mai kai hari na Sweden da ke taka Leda a Sporting, Victor Gyokeres mai shekara 26, da kuma dan wasan gaba na Kamaru mai taka leda a Brentford Bryan Mbeumo, Mai shekara 25.(L'Equipe)

Napoli ta shiga zawarcin Dan wasan Ingila kuma na gaban Manchester United Marcus Rashford Mai shekara 27.(Sun),

Har wayau, Napoli na da kwalin gwiwa kan dauko dan wasan Manchester United, Alejandro Garnacho, 20, Tuni ya yi wa dan wasan na Argentina tayin kwantiragin shekara 5. (Il Mattino)

Sai dai Serie A za su gafarta da kumgiyar side Tottenham kan dauko dan wasa Garnacho. (Football Transfers)

Brighton na son dauko dan wasan tsakiya na Ingila, Tosin Adarabioyo, 27, wa da ya koma taka Leda a Chelsea a watan Yuli. (Mail)

Deportivo La Coruna ya ki amince da tayin da Chelsea ta yi kan dan wasan Sifaniya turned Yeremay Hernandez. (Metro)

Kungiyar kwallon kafa ta City da ke gaba da Manchester City, na tattaunawa kan dauko dan wasa Jumq Bah mai shekara 18, wanda ke zaman bashi Real Valladolid daga AIK Freetong, a can kasar sa Saliyo (ESPN)

West Ham na son rage asara kan dan wasan Brazil Luis Guilherme, mai shekara 18, in da su ke son saida dan wasan gaban da suka siya watanni 7 da suka gabata.(Times)