Liverpool: Mohamed Salah na son yin ritaya a Anfield

An wallafa

Mohamed Salah ya ce yana son karkare sana'arsa ta tamaula a Liverpool.

Dan wasan tawagar Masar, mai shekara 29 ya ci kwallo 137 a wasa 214 da ya yi wa Liverpool, tun bayan da ta dauko shi daga Roma kan kan fam miliyan 34 a 2017 har da 12 da ya ci a kakar bana.

Kawo yanzu kwantiraginsa zai kare a karshen kakar badi a Liverpool.

''Ba daga waje na bane, amma idan aka tambayeni, zan so na ci gaba da taka leda a Liverpool har lokacin da zan yi ritaya. Amma makomar ba ta hannu na tana ga kungiyar sai abin da take bukata,'' kamar yadda Salah ya sanar ya Sky Sports.

Ya kara da cewar ''Kawo yanzu ban jin zan buga wasan da zan fuskanci Liverpool a wata kungiyar. Abu ne mai wahala, bana son jin wannan maganar, domin batun kan bata min rai.''

Salah ya fara taka leda a Al Mokawloon da ke garinsu daga nan ya koma Basel sai kuma Chelsea daga nan ya je Fiorentina sai Roma, sannan Liverpool ta dauke shi.

Liverpool za ta ziyarci Manchester United a gasar Premier League ranar Lahadi, inda ake sa ran Salah zai ci kwallo a wasa na 10 a jere.