Isra'ila ta dakatar da sakin fursunonin Falasɗinawa har sai abin da hali ya yi

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Sebastian Usher
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Middle East correspondent
- Aiko rahoto daga, Jerusalem
- Marubuci, Lucy Clarke-Billings
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Aiko rahoto daga, London
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Isra'ila ta ce ta dakatar da sakin fursunonin
Benjamin Netanyahu ya ce za su dakata da sakin fursunonin har sai sun samu tabbacin Hamas za ta ci gaba da sakin Isra'ilawa da ke hannunsu - kuma ba tare da gudanar da bikin sakinsu da ake gabatar da su a idon duniya, kamar yadda Hamas ke yi duk mako.
A zagaye na farko na musayar fursunonin, saura musaya ɗaya kawai take rage, wanda za a kammala a ranar 1 ga watan Maris.
Ba a ayyana ranar da za a fara zango na biyu na musayar fursunonin ba.
Ya kamata a ce wakilan Isra'ila da Hamas sun zauna ne domin tattaunawa tare da amincewa da yadda za a cimma yarjejeniyar zango na biyu na musayar - amma har yanzu ba su zama ba.
Masu shiga tsakani za su yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da cewa yarjejeniyar ba ta samu tsaiko ba, bayan dukkan ɓangarorin Hamas da Isra'ila sun zargi juna da ƙoƙarin karya yarjejeniyar.
Netanyahu ya zargi Hamas da karya yarjejeniyar, ciki har da amfani da fursunonin domin "farfaganda."
A nata ɓangaren, wani jami'in Hamas, Izzat al-Rishaq ya soki matakin Isra'ila na dakatar da sakin fursunonin a wata sanarwa da ya fitar a safiyar Lahadi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya ce batun Isra'ila cewa bikin miƙa fursunonin cin fuska ne, "hujja ce maras tushe," da suka ƙirƙira saboda kawo tsaiko a yarjejeniyar.
Sanarwar Netanyahun na zuwa ne bayan sako Isra'ilawa a ranar Asabar - Tal Shoham, Omer Shem Tov, Eliya Cohen da Omer Wenkert.
Sauran su ne Avera Mengistu da Hisham al-Sayed, waɗanda aka yi garkuwa da su a Gaza na tsawon shekaru - Mr Mengistu tun a 2014 da Mr al-Sayed wanda aka yi garkuwa da shi tun a 2015.
A musayar ce aka yi tsammanin sakin fursunonin Falasɗinawa 602. Hamas ta zargi Isra'ila da jan ƙafa wajen sakin fursunonin.
Fursunoni Isra'ilawa shida da Hamas ta saki su ne na ƙarshe a cikin waɗanda za a saka masu rai a zangon farko na yarjejeniyar.
A ɗayan ɓangaren, a kusa da gidan yarin Ofer da ke yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, Falasɗinawa da dama sun taru domin tarbar ƴanuwansu da za a sako.
A cewar hukumomin Falasɗinawa, fursunoni 50 ya kamata a sako waɗanda suke zaman ɗaurin rai da rai, 60 kuma suke da ɗauri mai tsawo, sannan akwai 445 da Isra'ila ta kama tun bayan harin 7 ga Oktoban 2023.
Akwai kusan Isra'ilawa 62 da Hamas ta yi garkuwa da su a ranar ta 7 ga Oktoban 2023, waɗanda ake tunanin kusan rabinsu suna da ransu.
Hamas ta fara sakin waɗanda ta yi garkuwa da su ɗin ta hannun Red Cross, domin musayar su da fursunoni Falasɗinawa a cikin yarjejeniyar tsagaita wuta.
Sai dai bayan an fara musayar, Hamas ta fara bikin sakin fursunonin, wanda ake nunawa kai-tsaye.

Asalin hoton, Reuters
A ranar Asabar ne aka saki Sholam mai shekara 40 da Mengistu mai shekara 39 ta hannun Red Cross a garin Rafah da ke kudancin Gaza, su kuma suka miƙa su da rundunar tsaron Isra'ila, IDF.
Hamas ta kama Sholam da matarsa da ƴaƴansa biyu ne lokacin da ya ziyarci ƴanuwansa da garin Kibbutz Be'eri a watan Oktoban 2023. An saki iyalansa ne bayan kwana 50.
Shi kuma Mengistu, wanda ɗan asalin Habasha ne mazaunin Isra'ila, an yi garkuwa da shi ne a watan Satumban 2014 lokacin da ya shiga arewacin Gaza.
Shi da Mr al-Sayed, wanda Balarabe ne ɗan Isra'ila sun kasance cikin waɗanda Hamas ta kama, amma sai aka saki al-Sayed cikin sirri a Gaza.

Asalin hoton, Reuters
Nuseirat da Shem Tov da Cohen da Wenkert duk an sake su a wurin bikin sakin fursunonin da Hamas ke yi.
Dukkansu an yi garkuwa da su a wajen taron kalankuwar Nova.
Da farko Shem ya tsere, amma ya dawo domin neman abokansa, wanda hakan ya sa Hamas ta rutsa da shi.

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Shutterstock

Asalin hoton, Reuters
Sauran waɗanda aka yi garkuwa da su ɗin da ake tsimayinsu sun haɗa da wani matashin soja mai suna Edan Alexander mai shekara 21.
Mahaifyarsa, Yael Alexander, wadda ta kalla bikin sako fursunonin, ta shaida wa BBC cewa, "abin farin ciki ne yadda ake sako su," amma ta ƙara da cewa iyalanta suna cikin damuwa.
"Akwai gomman fursunonin da suka da ransu, ciki har da ɗana, wanda muke sa ran za a sake shi. Burina kawai a sako min shi ya dawo daga Gaza."
Kusan mutum 1,200 ne Hamas ta kashe a harin na 7 ga Oktoban 2023, sannan ta yi garkuwa da 251.
Da Isra'ila ta ƙaddamar da martani, ta kashe aƙalla Falasɗinawa 48,319 ne, kamar yadda ma'aikatar lafiyar Hamas ta bayyana.










