Amorim ya ce zai tattauna da Garnacho kan abin da ya yi bayan canjinsa a wasa

Garnacho na tafiya ɗakin sauya kaya

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kociyan Manchester United Ruben Amorim ya ce zai tattauna da Alejandro Garnacho bayan da ɗan wasan gefen na gaba ya zarce kai tsaye zuwa ɗakin sauya kaya lokacin da aka canza shi a kashin farko na wasan da Utd ta doke Ipswich 3-2, jiya Laraba.

Amorim ya canza ɗanwasan na tawagar Argentina da ɗanbaya Noussair Mazraoui minti biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci bayan da alƙalin wasa ya ba wa Patrick Dorgu jan kati.

A lokacin ana zabga ruwan sama a filin wasan na Old Trafford, kuma Garnacho kusan ya nuna alamun cewa yana son ya je ya cire jesinsa saboda haka kai tsaye ya tafi ɗakin sa jesi maimakon ya je ya zauna a benci.

Ba a sani ba ko ya je ya zauna a bencin a bayan an koma daga hutun rabin lokaci.

"Zan yi magana da Garnacho a kan abin da ya yi," in ji Amorim.

A watan Disamba an cire ɗanwasan mai shekara 20 daga jerin waɗanda za su taka leda a karawar hamayya da Manchester City a Etihad tare da Marcus Rashford, kusan saboda baya kan ganiyarsa da kuma halayyarsa a lokacin.

Ba kamar Rashford, ba wanda bai sake yi wa United wasa ba tun daga lokacin kuma a yanzu ya tafi aro Aston Villa, Garnacho ya yi nasarar sake komawa cikin tawagar farko ta 'yanwasan ƙungiyar ba da ɓata wani lokaci ba.

"Kana abu irin na Rashford," in ji Amorim, da yake magana a kan abin da ya faru ranar Laraba.

Canjin da Amorim ya yi a lokacin ya yi shi ne a matsayin wata dabara saboda korar Dorgu da aka yi daga wasan, ta yadda zai ci gaba da tsarinsa na 'yanwasa biyar a gaba uku a tsakiya ɗaya a baya.

Amorim ya ce dole ne ya su zaɓi wanda zai fita.