Me ya sa Amurka za ta bai wa Isra'ila manyan makaman kariya a yanzu?

Asalin hoton, AFP via Getty Images
- Marubuci, Tom Bateman
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin Harkokin Wajen Amurka
- Aiko rahoto daga, Washington DC
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Fadar tsaron Amurka ta Pentagon ta tabbatar da cewa za ta aika makaman kare sararin samaniya masu cin dogon zango da kuma dakarunta zuwa Isra'ila.
Hukumomin sun ce makamin Terminal High-Altitude Area Defense (Thaad) za su taiamaka wa tsaron Isra'ila bayan harin da Iran ta kai mata a farkon watan nan.
Shugaba Joe Biden ya ce manufar ita ce "kare Isra'ila", wadda ake sa ran za ta rama harin da Iran ɗin ta kai mata da makamai masu linzami 180 ranar 1 ga watan Oktoba.
Matakin ya jawo hankali saboda ganin an ce za a haɗa da dakarun sojin Amurka zuwa Isra'ila.
Da ma akwai tsirarun sojin Amurkar a can - amma wannan rukunin na kusan soja 100 na da girma sosai saboda yadda yake ƙara nuna saka hannun Amurka wajen faɗaɗa yaƙi a Gabas ta Tsakiya.
Ana kuma ci gaba da ɗiga ayar tambaya kan irin ƙarfi ko amfanin da makaman kariya na Isra'ila ke da shi yayin da rikicin ke ci gaba da ruruwa.
Iran ta ce ta kai wa Isra'ila harin ne saboda kashe shugaban ƙungiyar Hezbollah Hassan Nasrallah da ta yi a birnin Beirut na Lebanon, wadda ƙawar Iran ce sosai.
Har yanzu babu tabbas ko tura makaman na cikin shirin Amurka na ko-ta-kwana wajen gyara ɓarakar da aka lura da ita bayan harin Iran, ko kuma dai hakan na nufin Isra'ila na shirin kai wa Iran ɗin mummunan hari ne.
Shugaba Biden ya nuna adawa da kai wa cibiyoyin nukiliyar Iran hari, da kuma na makamashin man fetur ɗinta, yayin da ake fargabar hakan zai iya haddasa babbar fitina kuma ya shafi tattalin arzikin duniya.
Duk ma abin da ya sa aka ɗauki matakin, hakan na nuna buƙatar taimakon Amurka da Isra'ila ke da ita yayin da yaƙi ke ruruwa a yankin.

Asalin hoton, Reuters
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Iran ta yi amfani da makamai kamar Fattah-1 da suka fita daga sararin samaniyar duniya kuma suke sassauya hanya kafin su auka wa inda aka harba su. Ɗaya daga cikin amfaninsu shi ne yadda suke da ɗankaren gudu fiye da na jirage marasa matuƙi da kuma ƙananan rokoki.
Makaman kariya na Thaad na da ƙarfi sosai da tare irin waɗannan makaman, a cewar kamfanin da ya ƙera su Lockheed Martin, wanda kuma shi ne mai ƙera makamai mafi girma a Amurka.
Wani kamfanin mai suna Raytheon na Amurkar ne ke ƙera na'urar bibiya ta makamin.
Ana amfani da makaman ne a kan na'urarorin da ke kan manyan motoci shida, inda yake ɗauke da kawuna takwas a kan kowacce. Kuɗinsa ya kai kusan dala biliyan ɗaya kuma yana buƙatar dakaru kusan 100 da za su dinga sarrafa shi.
Ana yawan neman makamin na Thaad, musamman Ukraine da ke neman daƙile hare-haren Rasha.
Saudiyya ta ba da odarsa tare da neman ƙari a matsayin alfanun da za ta samu daga Amurka idan ta kyautata alaƙa da Isra'ila - a wata yarjejeniyar gyara alaƙa da ta taɓarɓare bayan hare-haren 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai Isra'ila.
Harin da Iran ta kai na ranar 1 ga watan Oktoba ya kashe mutum ɗaya a Jericho da ke yankin Falasɗinawa da Isra'ila ta mamaye bayan ɓaraguzan ɗaya daga cikin makaman da aka kakkaɓo sun zubo masa.
Isra'ila na da makaman kariya da ake yawan kuzuzutawa, waɗanda Amurka ta samar, ciki har da Arrow 2, da Arrow 3.
Masu haɗa su a Isra'ila sun ce Arrow "ya yi aiki yadda ake so" wajen kakkaɓe makaman Iran.
Amurka ma ta taimaka wajen kakkaɓe makaman ta hanyar harba nata daga jiragen ruwa biyu a gabashin Baharrun, da kuma taimako daga wasu ƙasashen Turai da na Larabawa.
Amurka na nuna cewa harin na Iran "bai yi nasara ba".
Amma kuma ɓarnar da aka gani ta fi abin da ake faɗa. Hotunan da aka ɗauka na tauraron ɗan'adam sun nuna ɓarnar da harin ya yi a sansanin sojan sama na Nevatim da ake ajiye jiragen saman yaƙi na F-35, inda aka ga ramuka a kan tiitunan jirgin.
Decker Eveleth na cibiyar Center for Naval Analyses (CNA) ya ce hotunan sun nuna wuraren da makaman suka lalata aƙalla 32, ciki har da wurare da yawa a ma'ajiyar jiragen F-35.
"Wasu jiragen F-35 ɗin sun yi matuƙar sa'a," in ji Mista Eveleth a dandalin X.
An samu ɓarna a wurare da yawa, ciki akwai birnin Tel Aviv. Wani makamin ya haƙa rami mai zurfin ƙafa 30 a kusa da gidajen mutane amma kuma kusa da hedikwatar hukumar leƙen asiri ta Mossad.
Amurka ta tura sama da tan 50,000 na makamai zuwa Isra'ila cikin shekara ɗaya, a cewar alƙaluman hukumomin Isra'ilar.
Amurka ta yi ta kiran a koma kan teburin tattaunawa da farko, amma daga baya sai ga shi ta goyi bayan babbar ƙawarta Isra'ila ta hanyar ba ta kariyar siyasa da kuma makamai.
Isra'ila ta ce tana ci gaba da kai wa Hezbollah hare-hare a Lebanon da zimmar karya lagonta ta hanyar lalata makaman rokar da take harba mata tun daga ranar 8 ga watan Oktoban 2023 - bayan harin Hamas.
Hezbollah ta ce tana taya Falasɗinawa yaƙi ne kuma ba za ta daina ba har sai an cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta.
Amurka ta ce tura makaman Thaad wani mataki ne "babba da rundunar sojin ƙasar ta ɗauka a watannin nan" domin taimaka wa Isra'ila da kuma kare dakarun Amurkar daga hare-haren Iran da ƙungiyoyin da take taimakawa.
Ta ce an taɓa kai makaman Thaad kudancin Isra'ila domin atasaye a 2019, kuma shi ne lokaci ɗaya kuma na ƙarshe da aka san sun je wurin.
DA wuya a ga Amurka ta tura dakaru Isra'ila ba don yin atasaye ba, saboda ƙarfin Isra'ilar kanta.
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya yi gargaɗi a ranar Lahadi cewa Amurka na jefa rayuwar dakarunta "cikin haɗari ta hanyar tura su Isra'ila don sarrafa na'urorin kariya".











