Ko shan ruwan mama na da alfanu ga mazan da ba jarirai ba?

Hoton wata mata riƙe da ruwan mama a cikin roba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ruwan mama na taimaka wa jarirai wajen gina jikinsu har su girma kuma su ma manyan maza ma na amfana da shi
    • Marubuci, Sofia Bettiza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar Ɓangaren Lafiya
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

An fi saninsa da "zinare." Wasu ƙwararru sun ce wani abu ne da yake "ƙara ƙarfi."

Masana kimiyya sun amince cewa ruwan mama yana gina jikin jarirai da kuma kare garkuwar jikinsu daga cutuka. Sai dai wasu manyan maza na tunanin cewa su ma za su iya amfana da ruwan nonon.

Jameson Ritenour, mai shekara 39 da ke da ƴaƴa uku, ya ɗanɗani ruwan nono karon farko lokacin da abokiyar zamansa Melissa ke shayarwa - kuma take fitar da ƙarin ruwan maman da ba ta so.

"Na saka ruwan nonon cikin wata roba, duk da cewa abu ne da ba a saba gani ba," kamar yadda ya faɗa wa BBC.

Jameson ya zaƙu don sanin irin alfanun da ruwan mama ke ɗauke da shi bayan da ya kalli wani bidiyo a dandalin YouTube - inda wani mai motsa jiki ya yi magana kan tasirin shansa.

"Katon mutum ne," in ji Jameson.

Hoton Jameson Ritenour lokacin da yake motsa jiki ta hanyar ɗaga abubuwa masu nauyi

Asalin hoton, Jameson Ritenour

Bayanan hoto, Jameson Ritenour ya yi imanin cewa ruwan nono yana ƙara masa kuzari wajen motsa jiki - duk da cewa ƙwararru sun ce ya kamata a yi kaffa-kaffa

Shan ruwan mama na abokiyar zamansa ya zama wani ɓangare na abin yau da kullum a wajensa: Yana samun jaka biyu a rana, wanda ya kai kusan nauyin giram takwas.

"Jikina yana cikin yanayi mai kyau wanda ban taɓa kasancewa ba cikin rayuwata," kamar yadda ya faɗa wa BBC.

"Ruwan maman na taimaka min wajen gina jijiyon jikina. Ina rage ƙiba, yayin da nake samun ƙarin girman jijiyoyi da kashi biyar a cikin makonni takwas."

Jameson ya ce ya manta lokacin da ya kwanta rashin lafiya ko kuma ya shiga jin sanyi mai tsanani, tun lokacin da ya mayar da ruwan nono a matsayin ɓangaren abincinsa.

"Ina son na girma da kuma yi barci kamar jariri, don haka na yanke shawarar cewa nima zan ci kamar jariri," in ji shi. "Ina cikin koshin lafiya da kuma yanayi mai kyau."

Sayen ruwan mama ta intanet yana da hatsari

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Masana kimiyya sun ce babu wata hujja a kimiyyance da ta nuna cewa shan ruwan mama na da alfanu ga manyan maza.

Sai dai ƙwararru da ke kan gaba sun ce ruwan mama zai iya yi musu amfani, inda suka ce wasu bayanai da aka tattara sun nuna haka.

"Ruwan yana da sinadarai masu amfani da yawa - jariri yana samun girman jijiyoyi, kuma abin da masu motsa jiki ke buƙata kenan," a cewar Lars Bode, darektan cibiyar bincike kan ruwan mama a jami'ar California, a San Diego da ke Amurka.

"Masu motsa jiki na kula da jikinsu, don haka akwai abubuwa da suke so. Ba mu san yanda hakan yake ba a kimiyyance."

Sai dai Dr Bode ya ba da shawarar cewa a yi a hankali, inda ya ce ana samu masu sayan ruwan mama ta hanyoyi da akwai ayar tambaya a kansu kamar Facebook da Craigslist da kuma Reddit.

"Ba a yi wa irin ruwan maman gwaji, kuma akwai barazana ga lafiya," kamar yadda Dr Bode ya yi gargaɗi. "Za a iya samun nonon na ɗauke da cutuka irin HIV ko kuma ciwon hanta."

Ruwan nono yana kasancewa mai kyau da kuma lafiya ne kaɗai ga wadda take samar da shi, kuma zai iya kasance yana ɗauke da cutuka da dama.

Wasu matan da ke samar da ruwan maman na zaune ne a muhallai da ba a kula da su ko kuma waɗanda ba su iya haihuwa, don haka ruwan nonon zai iya ɗaukar wasu cutuka.

Wani bincike da wani asibitin kula da yara a Amurka ya yi a 2015, ya nuna cewa cikin ruwan nono da ake samu 101 a shafin intanet, kashi 75 yana tattare da cutuka - sannan kashi 10 kuma an haɗa shi da nonon saniya ko kuma wanda kamfanoni ke samarwa.

Hoton ruwan mama da aka aikawa Jameson Ritenour wanda ya saya ta intanet.

Asalin hoton, Jameson Ritenour

Bayanan hoto, Wannan ruwan mama ne da Jameson Ritenour ya saya a intanet. Ƙwararru sun yi gargaɗi kan sayan sa ta inanet

Bayan da James ya rabu da abokiyar zamansa kuma ta kai ba ya samun ruwan mama kamar yadda ya saba, ya yanke shawarar fara saya ta shafin intanet.

Ya ce ba shi da matsaniya kan barazanar da ke tattare da hakan.

"Na sayi ruwan nonon wurin wata da ban santa ba a kan intanet, sai dai na yi wasu bincike-bincike a shafin Facebook kuma na gano ba ta wata matsala," in ji Jameson. "Don haka na yanke shawarar amfani da damata."

Rashin isassun alkaluma bai dame shi ba, saboda ya ce ya san amfaninsa a wajensa.

Amma ya ce abin da yake ɗan damunsa shi ne tsangwamar mutane.

"Mutane na yi min wani irin kallo, saboda an fi sanin jarirai da shan ruwan mama. Sai dai ba wani abu bane kamar yadda mutane suke kallonsa."

Hoton wata mata tana shayar da jariri a China

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ruwan mama na taimaka wa jarirai wajen girma da kuma kare garkuwar jikinsu daga cutuka

Ya batun jarirai marasa galihu?

"Ba zan taɓa faɗa wa manyan maza su sha ruwan mama ba," in ji Dr Megan Azad, wanda yake bincike kan yadda ruwan mama ke taimaka wa lafiyar jarirai.

"Ba na tunanin zai yi musu lahani, sai dai akwai lahani da zai iya yi wa jariran da ke buƙatar ruwan mama - kamar bakwaini - da kuma waɗanda ke shan wahala wajen samunsa.

Dr Bode ya ce ya kamata a samar da isasshen ruwan nono ga jariran da ke buƙatarsa, maimakon a sayar don samun kuɗi.

"Ba mu da isasshen ruwan mama da za mu bai wa jarirai marasa galihu. Ruwan nono yana ɗauke da sinadarai da za su iya magance cutuka ga bakwaini. Zai iya ceton rayuka."

Dr Azad ya bayyana cewa idan uwaye suka yi tunanin cewa za su iya samun kuɗi ta hanyar sayar da ruwan nono a kan intanet, hakan zai ƙara barazanar batun sayar da ruwan mama ga maza da ke shansa.

Sai dai Jameson ya ce baya jin komai.

"Mutane sun zargeni da hana jarirai samun ruwan mama. Amma ba wai kamar ina tsaye a wajen asibiti bane, ina tambayar uwaye su ba ni dukkan ruwan nononsu!"

Ƙarin kan haka, ya ce kusan mata 100 ne suka tuntuɓe shi, inda suke ƙoƙarin sayar da ruwan mamansu.

Gano alfanun da ruwan nono ke da shi ga maza

Ruwan mama wani ɓangare ne da ba a yi bincike sosai kansa ba.

"A tsawon lokaci, mutanen da ke ɗaukar nauyin bincike ba su damu da ruwan mama ba, saboda suna kallonsa a matsayin wani batu na mata da ba shi da muhimmanci," a cewar Dr Azad.

Sai dai hakan na sauyawa.

Saɓani ga barazanar da ke tattare da shan ruwan mama da maza ke yi, yanzu ana gudanar da bincike don ganin ko hakan zai iya kasancewa waraka ga cutuka da dama da manya ke fama da shi, ciki har da ciwon zuciya da kansa da ciwon da ke kama gaɓoɓi da kuma cutar da ke shafar ciki.

Hoton ruwan mama.

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

Bayanan hoto, Robobin ruwan mama da aka ajiye a wani asibiti a Montevideo, da ke ƙasar Uruguay

Dr Azad yana cike da farin ciki, musamman kan yiwuwar samun alfanu da ruwan maman ke ɗauke da shi.

"Masu bincike na yin duba ko cewa za a iya amfani da ruwan mama wajen taimakawa manyan maza magance wasu cutuka," in ji Dr Azad.

"Mun san sinadarai da ke jikinmu suna da muhimmanci sosai ga lafiyar mu - don haka idan za mu iya gano sabbin hanyoyi na ƙara wannan alfanu, hakan zai kasance abu mai kyau. Kuma muna ganin za a iya samun haka a ruwan mama."

Wani bincike da aka wallafa a 2021, Dr Bode ya gano cewa ruwan mama yana rage cutuka da suka danganci jijiyoyi - abin da ke haddasa toshewar jijiyoyi da za ta kai ga bugun zuciya da shanyewar ɓarin jiki.

"Ruwan mama na da alfanun gaske," a cewar Dr Bode. "Shi ne abu kaɗai da mutane ke samarwa domin amfanin mutane.

Ya ce sinadarin ruwan nono ba shi da haɗari kuma ya fi aiki, ba kamar sauran magunguna da ake kirkirowa ba wanda mutane ke sha.

Amma yayin da ake ci gaba da bincike da kuma fata mai kyau, babu alkaluma isassu a ƙasa yanzu.

Idan bincike da ake yi ya samu nasara - wanda Dr Bode yake da ƙwarin gwiwa a kai - zai iya taka rawa wajen kauce wa kamuwa da bugun zuciya da kuma shanyewar ɓarin jiki, wadda ke janyo mutuwar miliyoyin mutane a faɗin duniya a kowace shekara.

"Ka yi tunani idan aka samu nasarar rage miliyoyin mutane da ke mutuwa sakamakon bugun zuciya da kuma shanyewar ɓarin jiki. Hakan zai zama babban ci gaba," in ji Dr Bode.