Kafar Barca ɗaya ta kai daf da karshe a Champions League

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kafar Barcelona ɗaya ta kai daf da karshe a Champions League, bayan doke Borussia Dortmund 4-0 a wasan farko zagayen kwata fainal ranar Laraba a Sifaniya.

Raphinha ne ya fara cin na farko sai Robert Lewandoeski ya kara biyu a jere da kuma Lamine Yamal da ya zura na huɗu a wasan.

Karo na biyu kenan da suka fafata a gasar zakarun Tutai ta bana, wadda aka sauya mata fasali.

Wannan shi ne karo na huɗu da suka kece raini a tsakaninsu a Champions League, inda Barcelona ta ci wasa uku da canjaras ɗaya.

Kakakr 2024/2025

Champions League ranar Laraba 9 ga watan Afirilun 2025

  • Barcelona 4 - 0 B Dortmund

Champions League ranar Laraba 11 ga watan Disambar 2024

  • B Dortmund 2 - 3 Barcelona

Kakar 2019/2020

Champions League ranar Laraba 27 ga watan Nuwambar 2019

  • Barcelona 3 - 1 B Dortmund

Champions League ranar Talata 17 ga watan Satumbar 2019

  • B Dortmund 0 - 0 Barcelona

Barcelona ta yi wasa 23 kenan a jere ba tare da an doke ta ba a dukkan karawa, tun shiga shekarar 2025.

Rabon da a doke Barcelona tun cikin Disamba, shi ne 1-0 da Atletico Madrid ta yi nasara.

Barcelona za ta je Jamus domin buga wasa na biyu ranar Talata 15 ga watan Afirilu.

Ƴ an wasan da suka buga wa Barcelona karawar: