Amurkawa na tambayar matsayin Elon Musk a gwamnatin Donald Trump

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Alex Lederman and Nomia Iqbal
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, in Erie, Pennsylvania
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
Tsoffin sojoji guda huɗu da suka haɗa da John da Jack da Bob da kuma Don ƴan shekaru kimanin 80 a duniya sun haɗu a teburi zagayayye a Erie da ke Pennsylvania domin tunawa da gomman shekaru da suka kwashe a matsayin abokai.
To sai dai akwai mutum na biyar wanda shi kuma ke da shekaru 70 wanda kuma yake shiga hirar tasu wato Shugaba Donald Trump.
Daga cikin mutum huɗun nan, Bob ne kawai ya zaɓi Donald Trump. To amma bayan ganin Elon Musk tsaye a kusa da shugaban Amurka a ofishin shugaban ƙasar wannan makon, lokacin da yake kare matsayinsa na rage ma'aikata da kashe kuɗaɗen gwamnati, Bob ya fara da-na-sanin zaɓar Donald Trump da ya yi.
"Ina shakkar sa," in ji Bob dangane da Musk. "Ina tunanin yana ƙoƙarin zama shugaban ƙasa ne."
Yankin Erie na ɗaya daga cikin wuraren da aka fafata da suka bai wa Trump damar cin zaɓe a 2024. Jam'iyyar Republican ta samu kaso 50.1 na ƙuri'un da aka kaɗa shekaru huɗu bayan abokin hamayyarsa Joe Biden na jam'iyyar Democrat ya tsira da ƙyar.
Ɗaya daga cikin alƙawuran da suka ja hankalin masu zaɓe suka zaɓi Trump shi ne yi wa tsarin aikin gwamnati garanbawul, inda ya sha alwashin rage ayyukan tiriliyoyi. Ƙuri'ar jin ra'ayin mutane ta nuna yadda alƙawarin ya ja hankalin ƴan Republican a lokacin kuma har yanzu abin da suke so ne.
Abin da bai fito fili ba ga masu zaɓe a lokacin kamfe shi ne irin rawar da Elon Musk zai taka a gwamnatin. Musk mai shekara 53 wanda shi ne mamallakin kamfanin mota na Tesla da shafukan SpaceX da X yanzu haka shi ne ke jagorantar hukumar da aka ɗorawa alhakin rage yawan kashe-kashen kuɗaɗen gwamnati kuma ana yawan ganin hotonsa tare da shugaba Trump.
Ƴan kwamitinsa na kutsawa ma'aikatu domin sanya ido kan yadda ake kashe kuɗaɗe sannan kuma sun kori miliyoyin ma'aikata. Sun kuma ɗaukin matakin dakatar da bai wa hukumomi kuɗaɗe da suka haɗa da ayyukan hukumomi kamar USAID a ƴan makonnin da suka gabata.
To sai dai bisa la'akari da irin ƙarfin faɗa-a-ji da Musk yake da shi a jaririyar gwamnatin Trump, ƴan jam'iyyar Democrats na nuna damuwa dangane da yadda za samu tangarɗa tsakanin aikin gwamnati da Elon Musk wanda kamfanoninsa ke da kwantaragin gwamnatin tarayya na biliyoyin daloli da ake ganin yana yi ne domin cin riba.
"Wannan babbar matsala ce. Wannan ya saɓa da muradan Amurka, "in ji Chuck Schumer, ɗan majalisar Democrat. "Kuma shugaba Trump na buƙatar ya nuna cewa zai iya jagoranci a fadar shugaban ƙasa kafin abin da suke yi ya rusa tsarin."

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shi ma John Pelinsky, tsohon ɗan jam'iyyar Democrat wanda a zaɓen watan Nuwamban 2024 ya dangwala wa Donald Trump ƙuri'a . Ya ce ƴan Democrat sun karkata ga tsauri sosai saboda haka yana son shekaru huɗun da Trump zai yi su "daidaita ƙasar".
Duk da cewa bai yi da-na-sanin zaɓar Trump ba, amma ya ce kasancewar Musk a kusa da Trump na tsorata shi.
"Yana tare da ɗansa a ofishin shugaban ƙasa," in ji shi. "Ban ji daɗin abin da ke faruwa ba."
"Ina tunanin ƙarfin faɗar da Musk ke da ita ka iya yin tasiri kan shugaban ƙasa," kamar yadda ya ƙara bayani. "Ina ganin abin da yake yi ya yi yawa. Ya kamata ya kasance da shafukansa na SpaceX da X da kuma kamfaninsa na motocin latironi."
Musk, dai bai ɓoye ba cewa yana aiki ne domin taya Trump ayyuka ga Amurkawa.
"Mutane sun zaɓi manyan sauye-sauyen gwamnati kuma abin da jama'a za su samu kenan, kamar yadda ya shaida wa ƴan jarida a lokacin wata ziyarar bazata da ya kai fadar White House a wannan makon. "Wannan shi ne dimokraɗiyya."
Wata ƙuri'ar jin ra'ayin ƴan AMurka da gidan talbijin na CBS News ya yi ya gano cewa mafi yawancin Amurkawa na ƙaunar aikin da Musk ke yi amma kuma ba su jin daɗin irin ƙarfin faɗa-a-jin da yake da shi.











