Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Har yanzu ba a ci Barcelona ba a waje a La Ligar bana
Barcelona tana mataki na uku a kan teburin La Liga, bayan da ta buga wasa na 25 a karshen mako.
Kungiyar da Xavi ke jan ragama, mai rike da kofin bara ta ci wasa 16 da canjaras shida, sannan ta yi rashin nasara uku kawo yanzu.
Ranar Asabar Barcelona ta je ta ci Celta Vigo 2-1 a wasan makon na 25, in da Robert Lewandowski ya ci biyu da kuma Iago Aspas ya zare daya.
Wasa na 12 da Barcelona kenan ta buga a bana a La liga a waje wadda har yanzu ba a doke ta ba, wadda ta ci karawa bakwai da canjaras biyar.
Real Madrid ce ta biyu da cin wasa tara da canjaras biyu aka doke ta karo daya, sai kuma Girona ta biyu da ta yi nasara takwas da canjaras uku aka doke ta wasa daya daga karawa a waje guda 12 a La Liga.
To amma a nahiyar Turai, Inter Milan ce ta daya, wadda ta yi nasara 10 da canjaras biyu a fafatawar waje, hakan ya sa take ta daya a teburin Serie A.
Wadda take ta biyu itace Bayern Leverkusen, wadda ta ci wasa tara da canjaras biyu daga fafatawa 11 da ta buga a waje a Buundesliga kawo yanzu.
Barcelona ce ta uku da kuma Paris St Germain cikin wadanda ba a ci ba a wasannin waje a kakar bana da suke taka leda.
Wannan ba shi ne karon farko da Barcelona ta yi irin wannan kwazon ba a wasannin waje, wadda ta yi hakan a 21/22 da kuma 22/23, inda ta yi karawa 19 a waje ba tare da an doke ta ba, wadda ta ci 13 da canjaras shida.
Wasannin da Barcelona ta buga a waje a La Liga kawo yanzu
Ranar Lahadi 13 ga watan Agusta 2023
- Getafe 0 - 0 Barcelona
Ranar Lahadi 27ga watan Agusta 2023
- Villarreal 3 - 4 Barcelona
Ranar Lahadi 03 ga watan Satumbar 2023
- Osasuna 1 - 2 Barcelona
Ranar Talata 26 ga watan Satumbar 2023
- Mallorca 2 - 2 Barcelona
Ranar Lahadi 08 ga watan Oktoban 2023
- Granada 2 - 2 Barcelona
Asabar 04 ga watan Nuwambar 2023
- Sociedad 0 - 1 Barcelona
Asabar 25 ga watan Nuwambar 2023
- R. Vallecano 1 - 1 Barcelona
Asabar 16 ga watan Disambar 2023
- Valencia 1 - 1 Barcelona
Alhamis 04 ga watan Janairun 2024
- Las Palmas 1 - 2 Barcelona
Ranar Lahadi 21 ga watan Janairun 2024
- Real Betis 2 - 4 Barcelona
Asabar 03 ga watan Fabrairun 2024
- Alaves 1 - 3 Barcelona
Ranar Asabar 17 ga watan Fabrairun 2024
- Celta Vigo 1 - 2 Barcelona
Wasan gaba da Barcelona za ta yi a La Liga
Ranar Asabar 24 ga watan Fabrairun 2024
- Barcelona da Getafe