Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Varane zai yi jinyar makonni a Man United
Dan wasan bayan Manchester United Raphael Varane ba zai yi jinyar wasu makonni saboda raunin da ya ji a karawar da suka yi da Nottingham Forest.
Varane, mai shekara 30, ya fita daga wasan a hutun rabin lokaci a wasan da United ta yi nasara da ci 3-2 a Old Trafford.
Majiyoyin kulob din sun yi watsi da batun da ake yi na cewa da zai yi jinya har na makonni shida, amma hutun wasannin kasa da kasa da ke tafe zai takaita yawan wasannin da United za ta buga ba tare da dan wasan ba.
Rashinsa ya kara maido hankali kan makomar Harry Maguire.
An yi tunanin cewa dan wasan na Ingila zai iya tafiya kafin a rufe kasuwar cinikin 'yan wasa ranar Juma'a, duk da cewa ya ki amincewa da tayin West Ham a farkon wannan watan.
Wannan da alama ba zai yuwu ba a yanzu, manyan masu tsaron baya da suka rage a United su ne Lisandro Martinez da Victor Lindelof da kuma Maguire.
Hakan na nufin kusan tabbas tsohon dan wasan bayan United Jonny Evans ya mai da kwantiraginsa na wucin gadi a halin yanzu zuwa na dindindin.