Wasan dusar ƙankara da ƙwallon Cricket na daga cikin hotunan Afirka na mako

An wallafa

Zaɓaɓɓun hotunan Afirka na mako da na 'yan nahiyar a wasu sassa na duniya

vv

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wasu ƙananan yara kenan ranar Lahadi a Laberiya lokacin da ƙasar ta karɓi baƙuncin shugaban adawa na ƙasar Guinea Cellou Dalein Diallo.
b

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani ɗan ƙasar Algeriya ke wasa cikin dusar ƙanƙara a kusa da tsaunin Aurès ranar Litinin
g

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Lahadi a wannan mutumin ke koya wa wani yaro wasan taya a birnin Johannesburg, na Afirka ta Kudu.
m

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wannan saniyar na kiwo a wata gona a arewacin Tunisiya ranar Juma'a.
g

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Lahadi kenan a Afirka ta Kudu lokacin da 'yan tawagar ƙwallon Cricket ta mata ta ƙasar Rwanda ke shirin fafatawa a gasar ƙwallon Criket da 'yan ƙasa da shekara 20 ta duniya da ake gabatarawa.
m

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Laraba ne kuma shugaban Adawa na Tanzaniya Tundu Lissu ya koma ƙasar bayan zaman gudun hijira na tsawon shekara shida da ya yi bayan da aka zarge shi da yunurin kisan kai
x

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Oluhle Siyo 'yar ƙasar Afirka ta Kudu ke atisaye gabanin karawa da ƙasar Sirilanka a gasar ƙwallon Cricket
g

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Talata 'yan ƙwallon rugby na ƙasar Kenya suka fafata a gasar rugby ta duniya da ake gudanarwa a ƙasar New Zealand.
x

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Nan wani kare ne a gidan adana namun daji na a birnin Alqahiran Masar