Waiwaye: Wawason kayan abinci a Kebbi da saka hannu kan dokar bai wa ɗalibai bashin karatu

An wallafa

Wannan maƙale ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi.

An daka wawar buhunan kayan abinci a Kebbi

Wasu mazaunan jihar Kebbi sun auka cikin wani gidan ajiyar kaya na gwamnati a unguwar Bayan Kara cikin Birnin Kebbi, inda suka wawashe buhunhunan kayan abincin da ke ciki.

Mutanen waɗanda suka bijire wa jami'an tsaron da aka jibge a gidan ajiyar, sun kuma fasa wasu gidajen ajiyar kaya na 'yan kasuwa da shagunan da ke yankin inda suka saci kayan abinci.

Jaridar Daily Trust ta kuma ruwaito cewa zauna-gari-banzan sun kuma far wa wata babbar mota da aka laftawa kayan abinci dangin hatsi waɗanda aka yi niyyar rabawa a Birnin Kebbi.

Ta ce wawar kayan abinci a gidajen ajiyar kaya irin na Birnin Kebbi, ta faru a Abuja da garin Suleja a cikin jihar Neja.

Hakan na faruwa ne yayin da ake fama da matsalar tsadar rayuwa wanda galibi aka yi imani ya faru ne sanadin cire tallafin man fetur da barin naira ta ƙwaci kanta a kasuwar canji.

Tinubu ya sa hannu kan dokar bai wa ɗalibai bashin karatu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya sa hannu kan dokar bai wa ɗalibai bashin karatu.

Ya sa hannu kan dokar ce a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Dokar mai taken kudurin sauya wa dokar bai wa dalibai rancen karatu fasali ta 2024, an samar da ita ne domin kafa asusun tallafa wa daliban manyan makarantu.

A watan Yunin 2023 ne dai shugaban ya fara rattabawa kudirin hannu to amma sakamakon wasu kurakurai da aka gano, ya sa ba a iya fara aiwatar da tsarin ba, inda shugaban ya sake mayarwa majalisa domin yin kwaskwarima.

Sabuwar dokar dai ita ce irinta ta farko a Najeriya kuma in ji shugaban ma’aikata na Fadar Shugaban Kasar Femi Gbajabiamila, wanda shi ne ya kawo kudurin dokar lokacin yana kakakin majalisa, za ta inganta kasar domin babu wani yaron Najeriya da za a hana wa damar samun ilmi mai zurfi saboda rashin kudi.

Ƴansanda sun tarwatsa ƴan Shi'a a Kaduna

An shiga ruɗani a Kaduna bayan da ƴan sanda suka yi kokarin tarwatsa mambobin kungiyar 'yan uwa Musulmi ta Islamic Movement Of Nigeria da ke karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Elzakzaky, wadanda ke gudanar da tattakin nuna goyon baya ga al'umma Falasdinu a tsakiyar birnin.

Bisa al'ada dai duk Juma'ar karshe ta watan Ramadan, 'yan uwa Musulmi na gudanar da tattakin domin nuna wa al'ummar Falasɗinu goyon baya dangane da irin "zaluncin" da suka ce ƙasar Isra'ila na yi musu.

Mambobin kungiyar sun taru a kan shatale-talen Katsina da ke kan titin Ahmadu Bello Way kafin ‘yan sanda su yi kokarin tarwatsa su.

Hakan ya janyo fargaba tsakanin mazauna birnin musamman ma waɗanda suke da shaguna a kusa da hanyar.

Manyan ɓarayi ma ba za su tsira ba a hannunmu - EFCC

Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ya tabbatar da cewa ba za su bar manyan ɓarayi ba a yaƙin da suke yi da masu alaƙa da cin hanci da rashawa a ƙasar.

Mista Ola Olukoyede ya ce ba za su bar kowa ba a aikin da suke yi. Ya ce a daidai lokacin da suke bin manyan ɓarayi, za kuma su ci gaba da bin sawun ƙananan ɓarayi.

Ya ce aikin da EFCC take yi zai ci gaba da karaɗe ko'ina, da kuma kan kowa da kowa ba tare da wani da ke alaƙa da duk wani nau'in laifin kuɗi ko na tattalin arziƙi ya kuɓuta ba.

Shugaban na EFCC ya ba da wannan tabbaci ne ranar Lahadi lokacin da hukumarsa ta shirya wani taron wayar da kai da kuma yunƙurin shigar da jama'a cikin harkokin yaƙi da cin hanci da rashawa.

A cewarsa, a cikin wata biyun da ya wuce, hukumarsa ta EFCC ta gurfanar da tsoffin gwamnoni guda biyu gaban shari'a.

Ana dai sukar hukumar ta EFCC da cewa ta zama kyanwar lami, ba ta iya bin manyan 'yan siyasa da sauran manyan masu riƙe da muƙaman gwamnati waɗanda ake zargi da tafka gagarumar sata da kuma almundahana da dukiyar al'umma.

Sai dai, Mista Ola Olukoyede ya ce ba gaskiya ba ne a ce EFCC ta fi kauri wajen kama masu damfarar intanet.

An kama mai sayar da yalo kan zargin yi wa yaro fyaɗe a Bauchi

Jami'an ƴan sandan jihar Bauchi da ke aiki ƙarƙashin rundunar maido da zaman lafiya sun kama matashi mai shekara 23 da ake zargin ya yi wa wani yaro ɗan shekara goma fyaɗe.

Matashin da ake zargi ya yaudari yaron da naira 30 da alawa inda ya nemi yaron ya raka shi wani kango da ke bayan wani gidan mai a kan titin Kofar Ran domin ya yi bahaya.

Sanarwar da kakakin rundunar ƴan sandan Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar ta ce bayan ya yi bahayar ne kuma, matashin ya buƙaci yaron da ya tuɓe wandonsa ya duba ko ya yi tsarki.

A cewar sanarwar, bayan da yaron ya cire wandonsa ne kuma, matashin ya cakumo yaron ta baya inda kuma ya yi masa fyaɗe.

Kotu ta samu Bobrisky da laifin wulaƙanta naira

Babbar kotu tarayya da ke Legas ta samu Idris Olanrewaju Okuneye da aka fi sani da Bobrisky da laifin wulaƙanta naira.

Alƙalin ya ajiye ranar yanke wa Bobrisky hukunci zuwa 9 ga watan Afrilu inda ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi a hannun EFCC.

Kafin samun sa da laifi, Bobrisky ya shaida wa kotu cewa ba shi da masaniya kan dokar hana wulaƙanta naira.

Alƙalin ya shaida masa cewa rashin sani ba hujja ba ne a doka.

Bobrisky ya kuma nemi alƙali da ya sake ba shi dama ta yin amfani da shafinsa na sada zumunta wajen ilmantar da mabiyansa game da illar yin liƙi da kuɗi.

"Ina da tarin mabiya fiye da miliyan biyar. Zan ɗora bidiyo a shafina kuma na faɗakar da mutane game da yin liƙi da kuɗi.

"Ba zan sake yi ba, na yi da na sanin abubuwan da nayi."

Bobrisky dai na iya fuskantar hukuncin wata shida a gidan yari ko biyan tarar naira dubu 50 ko ma ya yi duka biyun.