Saudiyya ta kunyata Argentina a Gasar Kofin Duniya

Asalin hoton, Getty Images
Argentina ta yi rasin nasara a hannun Saudi Arabia da ci 2-1 a wasan farko a rukuni na uku a Gasar Cin Kofin Duniya da suka kara ranar Talata a Qatar.
Minti 10 da fara wasa Argentina ta ci kwallo ta hannun Lionel Messi a bugun fenareti.
Kyaftin din Argentina ya zama na biyar da ya ci kwallo a gasa hudu a kofin duniya, wanda ya yi hakan a 2006 da 2014 da 2018 da kuma 2022.
Wadanda ke rike da tarihin wannan bajintar sun hada da Pele da Uwe Seeler da Miroslav Klose da kuma Cristiano Ronaldo.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Saudi Arabia ta farke ta hannun Saleh Al-Shehri, sannan minti hudu tsakani Salem Al-Dawsari ya kara na biyu.
Saudi Arabia tana ta 51 a jerin kasashen da ke kan gaba a taka leda a duniya kafin wasan da ta kara da Argentina, wadda take ta uku a jadawalin FIFA..
Kafin ranar Talata Saudi Arabia ta buga wasa 17 a Kofin Duniya da rashin nasara 11 da canjaras biyu da cin fafatawa uku.
Tawaga ukun da Saudi Arabia ta ci a Kofin Duniya sun hada da Masar a 2018 da Morocco da kuma Belgium a 1994.
Karon farko da Argentina ta yi rashin nasara a wasan da ita ke fara cin kwallo a Gasar Cin Kofin Duniya tun bayan 1958.

Asalin hoton, Getty Images
Argentina ta fara wasa a Gasar Kofin Duniya a Qatar ranar Talata, bayan karawa 35 a jere ba tare da an doke ta ba a dukkan fafatawa.
Ta fara wannan bajintar daga ranar 6 ga watan Yulin 2019, bayan doke Chile 2-1 a Copa America a Brazil.
Cikin kwazon da ya kai ta samun tikitin shiga Gasar Kofin Duniya a Qatar har da lashe Copa Ameria da cin wasa 24 da canjaras 11.
Wasa na 35 a jere da ba a doke ta ba shi ne wanda ta ci Jamaica 3-0 a karawar sada zumunta ranar 27 ga watan Satumba.
Argentina mai kofin duniya biyu ta yi ta uku a Gasar karo uku a 1930 da 1990 da kuma a 2014.
Haka kuma jumulla Argentina ta yi nasara a wasa 47 daga 81 a dukkan karawar Gasar Kofin Duniya a tarihi kafin wanda ta yi nasara a hannun Saudi Arabia..











