Me ya sa rikicin jihar Rivers ya ƙi ci ya ƙi cinyewa?

An wallafa

Alamu na ƙara nuna cewa da wuya a samu sulhu tsakanin tsohon gwamnan jihar Rivers kuma ministan Abuja, Nyesom Wike da gwamna mai ci, Siminalayi Fubara sakamakon rikice-rikicen siyasar da kullum ke ƙara raba kansu wanda har ya janyo rushe ginin majalisar dokoki sannan kwamishoni suka fice daga gwamnati yanzu kuma aka rufe ofisoshin shugabannin ƙananan hukumomi 23 na jihar.

A makon da ya gabata ne dai gwamna Siminalayi Fubara ya naɗa da rantsar da wasu mutum 23 a matsayin shugabannin ƙananan hukumomin na riƙon ƙwarya, duk da kin amincewar da tsoffin shugabannin ƙananan hukumomin suka yi na ƙin fita daga ofisoshin nasu.

Yanzu dai rundunar ƴan sandan jihar ta rufe ofisoshin ƙananan hukumomin inda ta hana dukkannin ɓangarorin shiga ofisoshin saboda abin da ta kira da "gudun tarzoma" da ke ƙara ruruwa a jihar.

Sabon rikicin siyasar jihar dai ya ɗauki sabon salo a ranar Talata, inda har ta kai ga an rasa rayukan mutum biyu da suka haɗa da ɗan sanda da wani farar hula mai zanga-zanga, kamar dai yadda rahotanni suka tabbatar.

Lamarin ya faru ne bayan da gwamnan jihar, Siminialayi Fubara, ya umarci shugabannin sassan mulki na ƙananan hukumomin 23 na jihar da su karɓi ragamar tafiyar da ƙananan hukumomin, bayan kammalar wa'adin shekara uku na ciyamomin a ranar Litinin.

Sakamakon tutsun da shugabannin ƙananan hukumomin suka yi ne ya sa matasa magoya bayan gwamnan mai ci suka gudanar da jerin zanga-zanga a sakatariyar ƙananan hukumomi guda uku na jihar, al'amarin da ya janyo rasa rayukan.

Su dai shugabannin ƙananan hukumomin waɗanda magoya bayan tsohon gwamnan jihar ne kuma ministan Abuja na yanzu, Nyesom Wike, sun ce ba za su bar mulkin ba bisa dalilin cewa ƴan majalisar dokokin jihar 27 da ke rikici da gwamnan, waɗanda suke biyayya ga Wike sun yi wa dokar wa'adinsu kwaskwarima, ta yadda za su ci gaba da zama a muƙamansu har wata shida bayan wa'adinsu.

Mene ne ke rura wutar rikicin?

Masana kimiyyar siyasa kamar Malam Kabiru Sufi, malami a kwalejin share fagen shiga jami'a ta Kano, ya ce abin da ya sa rikicin ya ƙi ci ya ƙi cinyewa ba zai rasa nasaba da dalili guda ɗaya ba mai alaƙa da ƙarfin mutane biyu wato tsohon gwamna da gwamna mai ci."

"Ƙarfin gwamna wanda ya bari wato Nyesom Wike wanda ya dasa muhimman abubuwa a jihar ciki har da gwamna mai ci. Sai shi kuma gwamna mai ci wato Siminalayi Fubara wanda yake da ƙarfin sauya al'amura ta hanyar rushe abubuwan da shi tsohon gwamnan ya kafa." In ji Malam Sufi.

Dangane kuma da ko yaushe ne rikicin zai ƙare, sai Malam Kabiru Sufi ya ce al'amarin zai ɗauki lokacin domin "haka za a yi ta tafiya har sai lokacin da ɗaya daga cikin mutanen ne biyu ya samu nasara a kan ɗaya. To a lokacin ne ɗaya zai saduda".

Wane ne ya kamata ya shiga tsakani?

Kawo yanzu dai da alama mutanen biyu ko dai ba sa sauraron manya a siyasa ko kuma waɗanda ya kamata su tsawatar musu ba su kai ga shiga su sasanta ba.

A watan Disambar 2023 ne shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya zauna da mutanen biyu wani abu da aka yi tsammanin zai kawo ƙarshen zaman tankiyar da mutum biyun ke yi.

Shi ma tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya fara wani yunƙuri na sasanta rikicin siyasar da ke ƙara kamari tsakanin Gwamnan, Siminalayi Fubara da mai gidan nasa Ministan Abuja Nyesome Wike yayin ƙaddamar da wani aiki da Jonathan ya je yi a jihar.

Jonathan ya ce dole ne jagororin biyu su ajiye bambance-bambacen da ke tsakaninsu saboda su yi aiki tare domin ciyar da jihar gaba.

Dr Kole Shettima, masanin kimiyyar siyasa ne a Najeriya ya shaida wa BBC cewa matakin da Jonathan ya ɗauka na sasanta Fubara da Wike na da alfanu.

Sai dai ya ce duk da amfanin hakan ba laile ne ya iya sasantasu ba.

"Na yi maraba da matakin da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya ɗauka na shiga maganar rikicin Wike da Fubara. Ko a wanne lokaci, ya kamata idan irin waɗannan abubuwan suka taso a samu dattawa da za su iya shiga tsakani, wataƙila a samu masalaha," in ji Shettima.

"Da yake Jonathan ɗan yankinsu ne kuma ya yi aiki tare da su, wataƙila ya samu nasara wajen sasanta su."

Masanin kimiyyar siyasar ya ce zai yi wuya a cimma wannan masalahar da ake so saboda alaƙar tsakanin Fubara da Wike ta yi matuƙar lalacewa.

Wace illa rikicin ke yi a kan jihar?

Malam Kabiru Sufi ya ce illar da rikicin na siyasa zai yi ga jihar ta Rivers ba shi da maraba da irin wanda sauran jihohin Najeriya masu fama da rikicin siyasa ke fuskanta.

"Na farko rikicin kan haifar da hamayya mai zafi a tsakanin 'yan jam'iyya guda ta yadda jam'iyyar za ta yi rauni ta kasa cimma abin a-zo-a-gani ga jama'a har wa'adinta ya ƙare.

Sannan a kan samu ƙaruwar 'yan bangar siyasa waɗanda da su ne ɓangarorin biyu ke amfani wajen yaƙar juna." In ji Malam Kabiru.

Ko rikicin zai iya kai wa ga dokar taɓaci?

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta sake yin kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sanya dokar ta-ɓaci a jihar Rivers saboda rikicin siyasar da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a cewarta.

Jam'iyyar ta buƙaci da a tura sojoji da makamai a girke su a wurare na musamman a jihar domin kare abin da ta kira ɓarkewar rikici.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa shugaban riƙo na jam'iyyar a jihar, Chief Tony Okocha, shi ne ya yi kiran a ranar Laraba a wani taron manema labarai a Fatakwal, babban birnin jihar yana mai cewa akwai alamu ƙarara na rashin bin doka da oda a jihar, wanda ya ce wasu da ba hukuma ba suna shiryawa.

To sai dai Malam Kabiru Sufi ya ce ba ya "tsammanin sanya dokar ta-ɓaci amma kuma lokaci ne kawai zai iya tantancewa".